Gwamna Yusuf ya fitar da gargaɗi ga ma’aikatan gwamnati bayan murabus ɗin Namadi






Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya fitar da gargaɗi mai tsanani ga dukkan jami’an gwamnati bayan murabus ɗin Kwamishinan Sufuri, Alhaji Ibrahim Namadi Dala, wanda ya yi murabus biyo bayan cece-kuce kan belin wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.





A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne yayin taron majalisar zartarwa na 30 da aka gudanar a gidan gwamnati a ranar Laraba.


Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani hali da zai lalata ƙimar da ta gina ba, yana mai cewa duk jami’in da ya kasa riƙe amana ya fi dacewa da ya ajiye aikinsa.




Ya ce yaƙi da miyagun ƙwayoyi da sauran munanan dabi’u na daga cikin ginshiƙan gwamnatinsa, tare da gargadin cewa duk wanda aka samu da hannu kai tsaye ko a kaikaice wajen irin waɗannan laifuka zai fuskanci hukunci.


Gwamnan ya kuma yi kira ga masu rike da mukamai su gudanar da ayyukansu bisa gaskiya, rikon amana da kima, domin kare mutuncin gwamnatin da suke wakilta.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT