Kungiyar matasan Najeriya Mai muradin wanzar da zaman lafiya da sasanta tsakanin ta rubutawa gwamnatin jahar lagas budaddiyar wasika.

 













Daga Ibrahim Abubakar Yola.



Kungiyar Northern Youth Peace and Reconciliation, ƙarƙashin jagorancin Ambasada A. A. Uba, ta fitar da budaddiyar wasika zuwa ga Gwamnatin Jihar Legas, tana mai kira da a biya diyya cikin gaggawa ga ’yan kasuwan Arewa da shagunan su aka rusa a kasuwar Alaba Rago da ke Legas.

‎Kungiyar ta bayyana cewa ’yan kasuwar sun fuskanci babbar asara sakamakon rushewar shagunan, don haka wajibi ne gwamnati ta ɗauki matakin biyan diyya da kuma samar musu da tsaro domin kare rayuka da dukiyoyinsu.

‎A cikin wasikar, kungiyar ta jaddada cewa:

‎ “Dan Najeriya nada yancin yin walwala da yin kasuwanci a kowanne yanki na ƙasar nan ba tare da muzantawa ko nuna wariya ba.”

‎Kungiyar ta yi gargadin cewa rashin daukar matakin gaggawa na iya haifar da rashin jin daɗi da kuma dagula zaman lafiya tsakanin al’umma.

‎Ta ƙara da cewa biyan diyya da samar da tsaro ga ’yan kasuwar zai zama alamar adalci da mutunta kowa a matsayin ɗan kasa.

‎Kungiyar Zaman Lafiya da Sulhu ta Matasa Arewa ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Legas da ta gaggauta biyan diyya da kuma samar da tsaro ga ’yan kasuwan Arewa da shagunan su aka rusa a Kasuwar Alaba Rago. Ta jaddada cewa kowa na da ’yancin kasuwanci a duk fadin Najeriya ba tare da wariya ba.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT