Majalisar Dokokin Jihar Gombe Ta Amince Da Kirkirar Sabbin Gundumomi 13
Daga: Zulqarnain Muhammad
Majalisar Dokokin Jihar Gombe ta amince da kudirin dokar da ke neman kirkiro sababbin Gundumomin Ci Gaban Kananan Hukumomi guda 13 (LCDAs) a fadin jihar, a wani mataki na karfafa shugabanci a matakin ƙasa da kuma gaggauta ci gaba a yankunan karkara.
Majalisar ta amince da kudirin ne yayin zaman zauren ta, bayan wani cikakken bincike da kwamitin kananan hukumomi da harkokin sarakunan gargajiya na majalisar ya gudanar.
A lokacin da yake gabatar da rahoton kwamitin, Mataimakin Shugaban Kwamitin, Hon. Musa Buba, ya bayyana cewa wannan mataki yana da nufin kusantar da gwamnati da jama’a, inganta isar da ayyuka da kuma karfafa shiga al’umma a harkokin gwamnati.
Ya kara da cewa kudirin ya kunshi tsarin aiwatarwa a matakai daban-daban, tsari na daukar ma’aikata da kuma tanadin kasafin kudi domin tabbatar da nasarar gudanar da sabbin Gundumomin.
Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Abubakar Muhammad Luggerewo, ya jinjinawa 'yan majalisa bisa sadaukarwar su ga ci gaban karkara tare da jaddada kudurin majalisar na samar da dokoki masu amfani ga jama'a.
Kudirin yanzu yana jiran amincewar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya domin ya zama doka.
Comments
Post a Comment