Mataimakiyar gwamnan jahar Adamawa ta mika yaran 14 da aka cetosu bayan safaransu da akayi zuwa kudancin Najeriya ga iyayensu.

 








Daga Alhassan Haladu Yola.


Gwamnatin jahar Adamawa ta mika Yara 14 wadanda aka cetosu daga hanun masu safaran mutane da akayi safaransu daga jahar Adamawa zuwa kudancin Nijeriya, ga iyayensu


Mataimakiyar gwamna Farfesa Kaletapwa Farauta ce ta mika yaran  ga iyayen masu a ofishinta harma ta baiyana takaicinta da aukuwar lamarin.





A cewarta  tun a watan 7  shekara ta 2025 ne dai gwamnatin ta samu bayanain sirri cewa akwai yaran da suka Bata  Wanda Kuma kananan Yara ne saboda haka sai aka shiga bincike Wanda hakan yasa aka tsare wata Mai suna Ngozi Abdulwahab.




Mataimakiyar gwamnan tace Ngozi ta dauki yaran da suke da shekaru daga 4-9 daga wurare daban daban dake fadin jahar Adamawa zuwa kudancin Najeriya Kuma tuninma ta sayar da Yara akan kudi nera dubi Dari takwaa N800,000 zuwa Milyon da digo bakwai N1.7. akan kowane yaro.




Ngozi da tana zaune ne a anguwar Jambutu dake karamar hukumar Yola ta arewa, wanda  take da karamin shago Kuma tana yaudaran yaran ne ta basu kauta.




Farfesa Farauta ta Kuma sanar da cewa kowane iyayen yaran da aka ceto an bashi nera dubi Dari da kayakin abinci dama Wanda bana abinciba domin samu saukin rayuwa.





Saboda haka nema take jadddada kiranta ga iyaye da sukasance suna kula da yaransu a Koda yaushe domin karesu daga shiga hanun masu safaran mutane.




Wasu daga cikin iyayen sun baiyana farin cikinsu dangane da ceton yaran tare da godewa gwamnatin jahar Adamawa bisa wannan na mijin kokari da sukayi na ceto musu yaran.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT