Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta sanar da tsintar yaro.
Daga Alhassan Haladu Yola.
An samu rahoton samun Wani yaro Mai shekaru 12 a takaice Kuma an sameahi ne a Wani wiri a karamar hukumar Gombi inda aka mikashi ga ofishin Yan sandan dake Gombi.
A cewar yaron iyayensa sun barshine a yolde pate dake cikin karamar hukumar Yola ta kudu.
Hakan na kunshene acikin wata sanarwa daga kakakin Rundunan Yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje Wanda ya rabawa manema labarai a Yola.
Sanarwa na Mai Kiran daukacin Al umma da cewa duk Wanda ya san iyayen yaron ko wadanda suke halaka da yaron da ya tuntubi ofishin kakakin Rundunan jahar Adamawa ko ofishin Yan sandan dake Gombi ko Kuma Akira wannan number waya. 08065470805
Allah ya sa Adace.
Comments
Post a Comment