Wata kungiyar Mai zaman kanta a jahar Adamawa ta kudiri aniyar wanzar da zaman lafiya.






Daga Alhassan Haladu  Yola.


Cibiyar wanzar da zaman lafiya, ilimi da Kuma cigaban Al umma dake jahar Adamawa Tasha alwashin inganta zaman lafiya da cigaban Al umma dama kare harkokin biladama a jahar dama kasa baki Daya.




Shugaban shurye shiryen cibiyar a jahar Adamawa Mr Sharif Wazir ne ya baiyana haka a zantarwarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.





Waziri ya tabbatar da cewa cibiyar tana aiki tukuru da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da kare hakkin Dan kasa da karesu daga duk Wani cin zarafi a cikin Al umma.




A cewarsa cibiyar ta lura cewa hakkin jama a na fuskantar kalubalen daga bangarori daban daban da suka hada da tsaro, sifiri da dai sauransu. Yace cibiyar zata gudanar da bincike domin ganin ba aci zarafin biladamaba.





Ya kirayi dukkanin Al umma da sukasance masu baiwa cibiyar hadin Kai da goyon baya domin ganin cibiyar ta cimma nasara wajen yaki da cin zarafin Yan Najeriya.




Waziri ya shawarci Yan Najeriya da sukasance masu bin doka, su Kuma kaucewa duk abinda zai karya doka, Mai makon haka suyi suka abinda zai wanzar da zaman lafiya, hada Kai dama zaman lafiya maidaurewa.




Haka Ka zalika cibiyar tana shirya gangamin wayarwa Al umma Kai dama ilimantar da Al umma domin su san yancinsu, dama yadda zasu kare yancin masu.




Waziri ya Kuma kirayi daukacin Al umma da kada su boye abinda yake damunsu su kaiwa cibiyar rahoton duk Wani cin zarafi da akayi musu, domin cibiyar a shirye take da take yancin Yan Najeriya baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT