YAR TAKARAN NEMAN KUJERAN KUNGIYAR NAWOJ TA KAI ZIYARA A FOMBINA FM YOLA.
Daga Alhassan Haladu Yola.
A yayinda ake daf da gudanar da zaben kungiyar Yan jarida bangaren mata a Najeriya NAWOJ shiyar jahar Adamawa,yar takaran neman shugabar kungiyar Felicia Dauda ta Kai ziyaran gangamin neman kuri a a gjdan Rediyo Fombina Fm Yola.
Felicia Wanda ta samu tarya daga ma aikata Maza da mata dake Fombina Fm Yola ta tabbatar da aniyarta na tsayawa takara shugabar kungiyar ta NAWOJ a zaben dake tafe.
Inda tace indan an zabeta zata kawo abubuwan cigaban kungiyar ba ga jaha kadaiba harma da kasa baki Daya. Kuma ta tabbatar da cewa zata Yi dukkanin abinda suka dace domin hadin kan Yan kungiyar dake kafafen yada labarain a fadin jahar ta Adamawa
Felicia ta Kuma nemi da a Bata jadinkai da goyon baya domin ganin ta Kai ga samun nasaran domin ta cimma burinta na Samar da hadin Kai da Kuma cigaban kungiyar.
Tunda farko ajawabinsa Babban darectan gangamin yaki nema zabenta Isuwa Ishaku ya baiyana godiyrsa da yadda aka karbesu hanu biyu biyu tare da cewa Yana Mai ganatar da yar takaran shugaban kungiyar NAWOJ da za a gurfanar Nan gaba kadan.
Saboda haka Yana neman hadin Kai da goyon bayan membobin kungiyar dake Fombina Fm Yola domin ganin sunkai ga samun nasara. Kuma yace yar takaran mace ce maikamar Maza wajen jajircewa wajen gufanar da aiyukan da zai kawo çigaba da hadin kai harma da zaman lafiya a tsakanin ya Yan kungiyar.
Itama anata jawabi sakatariya kungiyar Yan Jarida N U J shiyar Fombina Fm Yola Jawati Friday ta Yana tare da nuna goyon bayanta ga yar takaran Kuma tace baza su Bata kunyaba a zaben take tafe.
Hussani ya jinjinawa yar takaran bisa wannan ziyaran da ta kawo Kuma ya tabbatar mata da cewa kungiyar a shiyar Fombina a shirye suke su maramata baya domin ganin ta samu nasaran.
Da take magana a madadin Babban manajan Fombina Fm Yola Hajiya Zainab Umara shugaban sahin shirye shirye ta tabbatar da goyon bayanta ga yar takaran tare da kiranta da cewa in har ta samu nasaran to tayi aiki tare da kowa Kuma tayi dukkanin abinda zai kawo çigaba. Kungiyar ta NAWOJ domin su zama abin koyi.

Comments
Post a Comment