An bukaci mata da matasa suyi rijistan Katin zabe Wanda zai basu damar zabe a shekara ta 2027.





Daga Alhassan Haladu Yola.


An shawarci mata da matasa musammanma wadanda suka Kai matsayin yin rijostan Katin zabe da su hamzrya zuwa ofishin hukumar zabe domin yin rijistan Katin zabe Wanda zai basu damar yin zabe a shekar ta 2027.


Amiran Kungiyar mata Musulmai a Najeriya FOWAN shiyar Jahar Adamawa Hajiya Khadija Buba ce tayi wannan kira a Lokacin zantawarsa da manema labarai a Yola.



Hajiya Khadija ta Kara da cewa ga Wanda suka sauya wurin zama ko katinsu ya samu matsala da suyi kokari suje su gyara katinsu domin ganin sun gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsalaba.



Khadija Buba ta Kuma bukaci jama a da sukasance masu hakuri a lokacinda sukaje yin rijistan Kuma subi dukkanin Ka idodi da hukumar zaben ta gindaya Wanda hakan zai taimaka wajen basu damar yin rijistan yadda ya kamata.



Ta Kuma ahawar dukkanin masu ruwa da tsaki da Kara himma wajen wayarwa Al umma Kai dangane da yanka Katin zabe da Kuma baiwa hukumar zaben hadin Kai da goyon baya.



Har wa yau ta kirayi hukumar zaben Mai zaman kanta da ta Kara fadada cibiyoyin yin rijistan a dukkanin kananan hukumomin 21 dake fadin jahar ta Adamawa domin ganin duk wadanda suka canvanci mallakar Katin zabe sun samu Kati.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT