An shawarci Al umma da suje suyi rijistan Katin zabe.
Daga Alhassan Haladu Yola.
A yayinda Hukumar zabe Mai zaman kanta ta kasa INEC take cigaba da rijistan Katin zabe a fadin Najeriya an kirayi wadanda da suka cancanci yin rijistan dama wadanda suke da matsala da su gaggauta zuwa ofishin hukumar ki cibiyoyi da ake gudanar da rijistan da suyi rijistan katinsu Wanda shine zaibasu damar yin zabe a shekara ta 2027.
mashawarci na musamman kan harkokin jama a ga gwamna Ahmadu Umaru Fintiri Barista Sunday Wugira ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a Yola.
Barista Sunday Wugira yace Al umma su sani yin rijistan Katin zabe Yana da mutukan muhimmanci domin da shine zasu zabi ahugabannin da sukeso Kuma da shine zasu jaddada domokiradiya a Najeriya.
Saboda haka Barista yace Yana da muhimmanci jama a su garzaya ofishin hukumar zabe domin suyi rijistan, musammanma Wanda da suka Kai shekaru 18 dama wadanda basu da Kari ko suna da matsaloli, Kuma sukasance masu hakuri domin ganin kowa ya samu Katin.
Barista Wugira ya Kuma kirayi hukumar zabe wato INEC da tayi dukkanin abinda suka dace domin ganin kowa ya samu damar yin rijistan ba tare da wata matsalaba.
Ya Kara da cewa akwai bukatan hukumar zaben ta fadada cibiyoyin yin rijistan a fadin Najeriya, Wanda a cewarsa hakan zai taimaka ganin kowa ya samu yin rijistan akan lokaci.

Comments
Post a Comment