AN YABA DA YADDA JAM IYAR PDP TA GUDANAR DA ZABEN SHUWAGABANINTA DAGA MATAKIN ANGUWANNI ZUWA KANANAN HUKUMOMI. DAKE FADIN JAHAR ADAMAWA.
Daga Alhassan Haladu Yola.
An baiyana cewa zabukan shuwagabanin jam Iyar PDP daga matakin anguwanin zuwa kananan hukumomi ya gudana cikin kwanciyar hankali cikin lumana ba tare da matsalaba.
Barista Sunday Wugira mashawarci na musamman akan harkokin Al umma ga gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ne ya baiyana haka a zantawarsa da jaridar An Nur Hausa a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Barista Sunday Wugira yace zabunkan da jam Iyar PDP ta gudanar a jahar Adamawa abun a yabane don kuwa zaben an yishi ba da tashin hankaliba, bada tada hayaniyaba, zabe ne da akayishi bisa adalci, domin yiwa kowa adalci kamar yadda gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya bada umurnin ayi adalci ga kowa.
Barista Sunday ya kirayi sabbin shuwagabanin da sukasance masu adalci da rikon amana da hada Kai da fahintar juna domin ganin jam Iyar ta Kai ga samun nasara a zaben shekara ta 2025.
Barista ya Kuma shawarci membobin jam Iyar ta PDP da sukasance masu hada kansu da Kuma baiwa jam Iyar hadin Kai da goyon baya domin ganin jam Iyar ta ci zabe a shekara ta 2025.
Ya Kara da cewa Yana da yakimin cewa ya Yan jam iyara zasuyi iya kokarinsu wajen baiwa jam Iyar goyon bayan domin ganin ta cimma burinta na inganta rayuwar Al umma dake fadin jahar dama kasa baki Daya.
Barista Sunday yace biyo bayan gudanar da adalci da jam Iyar PDP ke dashi ne yasa aka gudanar da zaben shuwagabannin jam Iyar lafiya ba tare da tsangwamaba.
Harwayau Barista yace Jam Iyar itaace zata zatayi nasaran a zaben shekara ta 2025.

Comments
Post a Comment