GIDAUNIYAR BABBA INNA DA AWA PROGRAM TA SHIRYA BABBAN TARON MATA MUSULMAI A JAHAR ADAMAWA.
Daga Alhassan Haladu Yola.
Domin ganin an magance kalubalen rayuwa da Al umma Musulmai Ka fuskanta Gidauniyar Babba Inna Da awa Program ta shirya taron mata domin tattauna yadda za a shawo kan matsalar.
Taron Wanda ya gudanar a dakin taro na fadfatis dake cikin garin Jimeta a karamar hukumar Yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Malamai mata daban daban ne dai suka gudanar da jawabai iri iri a wurin taron. Malama Murnatu Ibrahim Duwan daga jahar Katsina ta gabatar da nata jawabinne akan hakkokin ma aurata, inda ta shawarci ma auratan da sukasance masu bin Ka idodin aure da Kuma mutunta juna domin Samar da zaman lafiya a tsakanin ma auratan yadda ya kamata.
Ta Kuma kirayi Al umma Musulmai da su kasance suna bada tasu gudumawar wajen hadin Kai da zaman lafiya a tsakanin ma aurata tare da kira musammanma ga matasa maza da mata da sukasance suna neman ilimin aure a Koda yaushe Wanda a cewarta hakan zai taimaka wajen daurewar aure.
T kare da cewa a rinka gudanar da bincike kamar yadda shariya ya tanadar domin kaucewa yawan sake saken aure a tsakanin Al umma Musulmai.
Malama Murjanatu ta shawarci iyaye da sukasance suna baiwa yaransu musammanma mata tarbiya dangane da zamanta kewar aure, Kuma sukasance masu hakuri da juna a Koda yaushe.
Malama Zainab Ja afar Mahmud Adam ta gabatar da nata jawabinne akan Sanya sutura da yamace Musulma ya kamata ta Sanya, inda ta kirayi mata Musulmai da sukasance suna Sanya suturan da zai rufe musu dukkanin Al auransu kamar yadda shariya addinin musulunci ya tanadar.
Malama Zainab Ja afar tace Yana da Muhimmanci ga ya mace musulma ta kasance tana Sanya suturan da zai kare martanarta da mutuncinta a idon jama a domin kaucewa aikata barna.
Malama Zainab tace Allah madaukakin sarkima ya bada umurni wajen Sanya sutura da ya kamata ga ya mace domin Samar da zaman lafiya.
Ta Kara da cewa Yana da kyau mata musamman ma na aure da sukasance sunayin adone a gidajensu ba wai a wajeba.
Itama ta kirayi iyaye da sukasance sunayiwa yaransu tarbiya dangane da Sanya sutura da ya dace tun suna Yara domin a cewarta hakan zai taimaka wajen dakile matsalar.
Ita kuwa malama Juwairiyya Usman Bauchi tayi nata jawabinne akan tasiri da Kuma illolin wayar hanu, malama ta shawarci matasa Musulmai Maza da mata, dama matan aure da su sanifa duk abinda sukeyi da waya ana sane da shi saboda haka ya kamata su san irin amfani da zasuyi da waya.
Malama Juwairiyya tace waya Yana da alfanu Yana da Kuma hatsari saboda haka su Maida hankali wajen yin amfani dashi ta yanyar da zai amfanesu domin kaucewa aikata laifuka ta waya.
Malamar dace Yana daga cikin illolin wayar hanu, yin karya, sata ko 419, yaudara nuna tsiranci, da dai sauransu.
Tace daga cikin muhimmanci waya sun Jada da yin karatu sada zumunta, yin kasuwanci da dai sauransu.
A jawabinta malama Khadija Buba Amiran Kungiyar mata Musulmai a Najeriya FOWAN shiyar Jahar Adamawa ta yabawa Gidauniyar Babban inna bisa shirya wannan taro tare da Kiran mahalarta Taron da suyi amfani da dukkanin jawabai da akayi domin neman tsira ranan gobe kiyama.
Ta Kuma godewa dukkanin malamai da suka gabatar da jawabai tare Yi musu Adu ar Allah madaukakin sarki da ya mayar dasu gida lafiya.
Hajiya Zaliha Justice AbdulAziz Waziri Wanda itacema ta shirya Taron ta godewa daukacin dukkanin wadanda suka halarci Taron, da ma kwamitin da suka jagoranci ganin Taron ya gudana yadda ya kamata.

Comments
Post a Comment