Kungiyar Tabbatar Pulaku Jamde Jam Foundation dake jahar Adamawa Tasha alwaahin wayar da Kai dangane da yin rijistan Katin zabe.
Daga Alhassan Haladu Yola.
An bukaci Al umma Fulani da su tabbatar da cewa suyi rijistan Katin zabe domin basu damar zaban shugaban da sukeso musammanma Wanda za taimaka musu wajen bunkasa harkokinsu na kiwo.
Mataimakin shugaban kungiyar Tabbital Pulaku Jamde Jam Foundation dake jahar Adamawa Hassan Ali Soja ne ya bada wannan shawara a zantawarsa da manema labarai a Yola.
Hassan Ali Soja yace yin rijistan Katin zabe Yana da matukan muhimmanci saboda haka Al umma Fulani kada su yarda abarsu a baya suyi amfani da wannan lokaci da hukumar zabe taka wato INEC ta fara yiwa Yan Najeriya rijistan Katin zabe musammanma wadanda suka cika shekaru 18 da Kuma wadanda suka samu matsala a katinsu na zabe.
Hassan Ali ya baiyana cewa zaiyi amfani da wannan damar wajen fadakar da Al umma Fulani musammanma wadanda ke yankunan karkara muhimmanci Katin zabe domin a cewarsa hakan shine kadai zai basu damar zaban shuwagabanin da sukeso a ransu.
Saboda haka kada suyi da wasa wajen halartan dukkanin cibiyoyin da hukumar zabe ta ware domin yin rijistan Katin zabe domin Suma suyi nasu rijistan, domin samun cigaba, harma da bunkasa domokirasiya.
Hassan ya Kuma kirayi Al umma Fulani da sukasance masu hakuri da bin Ka idodin hukumar zabe da zaran sunje yin rijistan Katin zabe.
Ya Kara da cewa kungiyar tasu zatabi lungu lungu da Sako Sako domin fadakar da Al umma Fulani dake fadin jahar dangane da yin rijistan Katin zabe. Saboda yadda aka fuskanci zaben shekara ta 2027.
Ya Kuma shawarci hukumar zaben da ya fadada cibiyoyin yin rijistan domin ganin kowa ne Dan kasa Wanda ya can canci rijistan katai yayi rijistan na tare da matsalaba.

Comments
Post a Comment