Majalisar addinin musulunci a jahar Adamawa ta zabi sabbin shuwagabanin da zasu shugabaninci majalisar na tsawon shekaru uku.
Daga Alhassan Haladu Yola.
Majalisar harkokin addinin musulunci a jahar Adamawa ta sake zaben sabbin shuwagabaninta da zasuja ragamar shugabanin majalisar na tsawon shekaru uku. Akasarin wadanda suka rike da mukami a majalisar sun koma kan mukamensu biyo bayan fahintar juna da Kuma amivewa da membobin majalisar sukayiwa shuwagabanin.
Alhaji Gambo Jika Wanda aka sake zabaanaa a matsayin shugaban majalisar harkokin addinin musulunci a jahar Adamawa, ya baiyana godiyrsa ga daukacin membobin majalisar bisa wannan hadin Kai da goyon baya da suka bashi, tare da kiransu da su cigaba da hada Kai domin samun cigaban majalisar addinin musulunci a fadin jahar ta Adamawa.
Ya Kuma tabbatar da cewa zaiyi aiki da kowa domin samun cigaban majalisar saboda haka yake kira ga daukin membobin kungiyar da su cigaba da yin dukkanin abinda suka dace domin cigaban majalisar.
Alhaji Gambo Jika ya jaddada aniyarsa na yin dukkanin Mai yiwa domin domin gudanar da aiyukan cigaban majalisar a fadin jahar dama kewaye.
A sakonsa na bukukuwar maulidi ya yi fatan Allah yasa a kammala bukukuwar lafiya tare da Kiran daukacin Al umma Musulmai da suyi koyi da halayen manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbatar a gareahi. Domin Samar da hadin Kai da wanzar da zaman lafiya.
Shima a jawabinsa shugaban kwamitin Shura Sheirk Musa Abdullahi Wanda kwamitin nema ya jagoranci zaben ya baiyana cewa an gudanar da zaben ne bisa amincewar dukkanin membobin majalisar, Wanda hakan ya bada damar dawo da wadanda ke rike da mukami kan kujeransu.
Sheirk Musa Abdullahi ya shawarci sabbin shuwagabanin da sucigaba da yin aiyukan cigaban majalisar harkokin addinin musulunci.

Comments
Post a Comment