MATA UKU SUN SAMU YANCI DAGA GIDAN YARI A JAHAR ADAMAWA.
Daga Alhassan Haladu Yola.
Babban Inna DA awa Program karkashin jagorancin Hajiya Zaliha Justice AbdulAziz Waziri ta Yanta mata uku bayan yanke musu hukunci a gidan yari dake jahar Adamawa.
Hakan ya biyo bayan ziyaran gidan yarin Wanda Hajiyar da tawaganta suka Kai a gidan yarin dake Yola.
Gidauniyar ta Babba Inna Da awa Program karkashin jagorancin Hajiya Zaliha AbdulAziz Waziri ta Yanta mata uku akan kudi nera dubu Dari 236 na Tara da akayi musu.
Haka Kuma gidauniyar ta taimakawa mazauna gidajen yarin da kayakin da suka hada da katon no omo biyar Dana sabulai, magunguna da dai sauransu.
Gidauniyar ta Babba Inna Da awa Program ta kudiri aniyar inganta rayuwar Al umma domin ganin an samu cigaba yadda ya kamata harma da wanzar da zaman lafiya a jahar da kasa baki Daya.

Comments
Post a Comment