An bukaci manoma a jahar Adamawa da sukasance suna Kai rahoton duk wasu cututtuka da suka gani a gonakainsu a ofishin ma aikatan gona dake kusa dasu.




Daga Alhassan Haladu  Yola.


 A Wani mataki na magance matsalolin cututtuka dake addabar amfanin gonakai an shawarci manoma da sukasance suna Kai rahoton duk abinda basu ganeba a gonakainsu zuwa ofishin ma aikatar gona dake kusa da su domin daukan matakin da ya dace akai.





Mashawarci na musamman akan harkokin noma da kananan sanao I ga gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa Alhaji Usman Abubakar Wanda akafi sani da Manu Ngurire ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.




Alhaji Usman Abubakar ya baiyana haka ne a lokacinda yake jawabi dangane yadda wasu cututtuka suka adabi Dawa a wasu kauyuka dake fadin jahar Adamawa.



Alhaji Manu yace Yana da muhimmanci manoma su Maida hankali sasai akan harkokin nomamsu da Kuma sanin me yake samun amfani da suka shuka acewarsa da sunga wata cuta na addabar gonakainsu to suyi gaggawar Sanar da hukumomin da abin ya shafa domin ganin an dakile cutar ba tare da samun wata asaraba.



Ya kuma koka da yadda wasu manoma sukeyun biris da cututtuka dake damun amfanin gonakainsu basa kaiwa hukumomin rahoton abinda yake damunsu. A cewarsa wannan lamarin Yana ci musu tuwo a kwarya.




Saboda haka nema yake kira ga babbar murya ga manoma dake fadin jahar Adamawa da sukasance suna kaiwa hukumomin rahoton abinda suka ga ba daidaiba a gonakainsu ga hukumar ma aikatar gona dake kusa dasu. Wadanda suka kama daga kananaan hukumomin har zuwa jahar.





A cewar Alhaji Usman dai gwamnatin jahar Adamawa karkashin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ta kimtsa tsaf domin kawo magungunan magance cututtuka dake damun gonai a fadin jahar .




Yace gwamna Fintiri ya kudiri aninyar ganin an bunkasa harkokin noma a fadin jahar Adamawa da zumar Samar da wadaceccen abinci, harma da samarwa matasa aikinyi.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT