ASUU shiyar jami ar Modibbo Adama tabi sahun takwarorinta wajen fara yajin aikin gargadi a Jami’ar Modibbo Adama, dake Yola
Daga Alhassan Haladu Yola.
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, reshen Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, ta fara yajin aikin gargadi na makonni biyu, bisa umarnin shugabancin ƙasa na kungiyar, kan wasu buƙatu da ba a warware tsakaninta da Gwamnatin Tarayya ba.
Shugaban ASUU na jami’ar, Comrade Modibbo Muhammed Buba, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan taron majalisar kungiyar da aka gudanar a jami’ar.
Comrade Buba ya ce sun ga ya dace su yi jawabi ga manema labarai domin su fayyace matsayinsu game da tattaunawar da suke yi da gwamnatin tarayya, da kuma sanar da jama’a game da matakin da majalisar zartarwa ta ƙasa ta ASUU ta ɗauka a ranar 29 ga Satumba, 2025.
Ya ce majalisar ta nuna damuwa kan yadda gwamnati ke sakaci da harkokin jami’o’i, tare da ƙin cika alƙawarin da ta dade tana yi. A cewarsa, gwamnati ta yi kunnen uwar shegu ga wa’adin kwana 14 da ASUU ta ba ta, abin da ya sa suka ɗauki matakin shiga yajin aikin gargadi na makonni biyu.
Sanarwar ta lissafa muhimman batutuwan da suka haddasa yajin aikin kamar haka:
Kammala tattaunawar yarjejeniyar ASUU da gwamnatin tarayya ta 2009 da aka sabunta.
Sakin albashin watanni uku da rabi da aka hana malamai.
Tabbatar da kudaden ci gaba da farfaɗo da jami’o’in gwamnati.
Daina cin zarafin malamai a LASU, Kogi (Prince Abubakar Audu University), FUTO, da sauran jami’o’i.
Biyan bashin ƙarin albashi na kashi 25 zuwa 35 cikin ɗari, da bashin matsayi na fiye da shekaru huɗu.
Sakin kuɗaɗen ɓangare na uku, ciki har da kuɗin haɗin gwiwa da harajin ASUU.
Kungiyar ta bayyana cewa sakataren dindindin na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ya roƙe su da su janye wa’adin da suka bayar, yana mai yabawa da haƙurin da suka nuna tsawon shekaru takwas da tattaunawar ke gudana.
Sai dai ASUU ta nuna takaici cewa duk da alƙawarin gwamnati, har yanzu ba ta gabatar da wani tayin tabbatacce ba.
Sanarwar ta tambayi cewa, “Ta yaya gwamnati da ta shafe shekara guda tana tattaunawa da tawagar ASUU za ta tsaya cak yanzu ba tare da wani mataki ba?”
Comrade Buba ya ƙara da cewa yadda gwamnati ke tafiyar da batun ya nuna rashin niyyar gaske, tare da jaddada cewa ƙin amincewa da yarjejeniyar da aka cimma na nuni da rashin mutunta tsarin ilimin jami’a a ƙasar.
Ya tabbatar da cewa ASUU za ta ci gaba da kare mutuncin jami’o’in gwamnati da kuma dorewar su.
Comments
Post a Comment