Hukumar Inshoran lafiya ta kasa ta yi yunkuri domin kawo karshen jinkirin bada jinya




Babangida Galleon 

 


Babban daraktan hukumar inshoran lafiya ta kasa NHIA, Dakta  Kelechi Ohiri, ya umirci ofisuin hukumar na jahohi da cibiyoyin kula da harkar lafiya HMO da su tabbatar ba ayi jinkirin sama da awa guda ba gurin kula da mara lafiya a duk wata asibiti da ke cikin tsarin inshorar lafiya da ke fadin kasa.



Jami'in kai komon hukumar na jahar Adamawa, Abdulhakim Aliuu ne ya fadi haka yayin taron masu ruwa da tsaki mau taken: FADADA DAMA, TABBATAR DA DAIDAITO  wanda ofishin hikumar na jaha ta shirya a birnin yola.


 Jami'in kai komon ofishin  hukumar inshorar lafiya ta kasa da jahar Adamawa Abdulhakim Aliyu  yace bada wannan umurnin na cikin jerin sauye sauye da babban daraktan  hukumar ke kawowa  wanda ke  baiwa marasa lafiya fifiko, ganin yanzo bukatar izinin bada jinya ba zai sake daukan lokaci ba gurin bada kiwon lafiya.




Abdulhakim yace matsalar karewan magani ya zo karshe a jahar Adamawa ganin yanzu asibitoci na bin dokokin hukumar kamar yadda ya dace kuna marasa lafiya ba du sayan magani a waje.



Yayin da babban daraktan ya kara jan  hankalin  gurin kulawa da wanda ke tsarin inshoran lafiya, ya kuma yi kira ga ma'aikata da su rika ziyarar asibitoci a koda yaushe domin sanin matsalolin da masu amfani inshoran  lafiyar ke fama da su,  kuma duk wani asibiti da aka samu da laifin kin cika ka'ida, za a ladabtar da shi.



Abdulhakim yace taron  masu ruwa da tsakin wanda shine na farko a wannan shelara ya zo a daidai ganin zai taimaka gurin samun karin ilimin aiyuka da na'ura mai kwakwalwa da babban daraktan ya kirkiro sabbi domin daidaita harkar ilimi.


Haka itama dakta Nneka Chinemeze,  wanda tayi jawabi kan yadda ake bi domin bin hakkokin kudaden asibitoci da suka bada jin ya dama yadda ake mika bukatar izinin jinya,  tace zaman zai bai wa asibitoci damar fahimtar yadda hukumar inshorar lafiya ta kasa ke gudanar da aiyukan ta, da kuma kawo karshen kurakuran da ake samu.


A nashi jawabi, shugaban hukumar kula da asibitoci na jahar Adamawa,  

 Dakta Amdzaranda Aidan wanda ya samu wakilcin daraktan bangare abinci da magunguna,  Famasis Hasiya Mohammad, yace zaman zai bawa masu ruwa da tsaki daman waiwaye adon tafiya domin duba nasarori da aka samu, kura kuren da ba za a rada ba, da kuma bukatar hada kai domin inganta harkar kiwon lafiya wa al'ummar jahar.


  Shugaban yayi kari da cewa hukumar kula da asibitocin jahar na shirye domin aikin tare da hukumar inshorar lafiya domin inganta kiwon lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT