Hukumar Kwastam ta Najeriya ta sake jaddada aniyarta na ƙara kaimi wajen yaƙi da fasa-kwauri a yankin iyakar Najeriya da Kamaru, domin ƙarfafa tsaron ƙasa da kuma bunƙasa tattalin arziki.
Daga Alhassan Haladu Yola.
Kwamptroller na Kwastam reshen Adamawa da Taraba, Garba B. Bashir, ne ya bayyana haka yayin da yake wa manema labarai jawabi a hedikwatar hukumar da ke Yola.
Ya ce cikin makonni shida da suka gabata, hukumar ta samu nasarar kama kaya har guda 29 da kudinsu ya kai naira miliyan ɗari ɗaya da goma sha biyu da rabi, sakamakon samamen da aka gudanar bisa bayanan leƙen asiri a wuraren da ake zargin fasa-kwauri.
Kwamptroller Bashir ya bayyana cewa an kama kayan ne a yankunan Mubi–Sahuda, Girei–Wuro Bokki, Jamtari–Farang/Belel, Wuro Alhaji, Damare bank, Gurin–Fufore da kuma hanyar Yerima a Gembu.
Kayan da aka kama sun haɗa da lita 20,600 na fetur da aka zuba a cikin jakan roba 824, kwalaye 91 na ƙwayar Tramadol da ta ƙare wa’adinta, kwalaye 54 na sabulai daga ƙasashen waje, da kuma fatar jakuna 64 da ake ƙoƙarin fitarwa ƙasar Kamaru ba bisa ƙa’ida ba.
Kwamptroller Bashir ya ce an kama ƙwayar Tramadol ɗin ne a ranar 30 ga Agusta 2025 a Mubi, a wani samame da sashen bincike ya jagoranta. Ya bayyana cewa hakan ya hana aukuwar annobar lafiya, duba da illar da irin waɗannan ƙwayoyi ke da ita ga matasa.
Ya nakalto rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wanda ke nuna cewa sama da mutane miliyan ɗaya ke mutuwa a duk shekara sakamakon shan magungunan bogi ko marasa inganci, inda Afirka ke ɗaukar mafi yawan asarar.
Kwamptroller ɗin ya ƙara da cewa za a mika ƙwayoyin da aka kama ga hukumar NAFDAC domin ɗaukar matakin da ya dace da lalata su, bisa tanadin Sashe na 55 na dokar Kwastam ta 2023.
Haka kuma, an kama fatar jakunan 64 a ranar 30 ga Satumba 2025 a bakin kogin Damare da ke jihar Adamawa, inda ake shirin fitar da su zuwa Kamaru, sabanin tanadin jerin kayayyakin da aka haramta fitarwa a jadawalin CET da sashe na 150 na dokar Kwastam.
A cewarsa, “yankan jakuna don fitar da fatar su yana barazana ga rayuwar jinsin dabbobin, don haka jami’anmu suka hanzarta dakile lamarin.”
Bugu da ƙari, hukumar ta kama kwalaye 54 na sabulai daga ƙasashen waje a bakin kogin Damare a ranar 3 ga Oktoba 2025. Bashir ya ce shigowa da irin waɗannan kayayyaki na saɓawa jerin haramta shigo da kaya da dokar Kwastam ta 2023.
Ya bayyana cewa fetur ɗin da aka kama za a sayar da shi ta hanyar gasa ga jama’a, kuma kudin da za a samu za a mika shi ga Asusun Tarayya.
Kwamptroller Bashir ya kuma jaddada cewa hukumar tana ci gaba da haɗin gwiwa da al’ummomin kan iyaka da sauran hukumomin tsaro wajen dakile fasa-kwauri ta hanyar musayar bayanai da tattaunawa.
“Mun kasance muna hulɗa da al’ummomin kan iyaka akai-akai domin su guji shiga harkar fasa-kwauri. Kwamitinmu ya kuduri aniyar karya duk wata hanyar da ’yan fasa-kwauri ke bi a jihohin Adamawa da Taraba,” in ji shi.
Ya kuma yaba wa Babban Kwamptroller Janar na Kwastam, Adewale Adeniyi, da tawagarsa bisa samar da yanayi mai kyau na aiki, tare da gode wa sauran hukumomin tsaro bisa haɗin kai.
Kwamptroller Bashir ya roƙi ’yan jarida da su ci gaba da wayar da kan jama’a game da illolin fasa-kwauri ga tattalin arziki da tsaron ƙasar.
Comments
Post a Comment