Jam’iyyar SDP ta rusa shugabancin ta na jiha a Adamawa, ta kafa kwamitin rikon kwarya na kwanaki 90





Daga Ibrahim Abubakar Yola.


Kwamitin Aiki na Ƙasa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ya rusa shugabannin jam’iyyar na jihar Adamawa, tare da kafa kwamitin rikon kwarya da zai kula da harkokin jam’iyyar a cikin watanni uku masu zuwa.


A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na ƙasa, Dakta Olu Agunloye, ya fitar mai ɗauke da ranar 9 ga Oktoba, 2025, an bayyana cewa matakin ya biyo bayan cikakken nazari da aka yi kan ayyukan jam’iyyar a jihar.


Sanarwar ta ce an ba wa sabon kwamitin rikon kwarya umarni da ya sake tsara tsarin jam’iyyar a jihar, ya ɗauki sabbin mambobi, tare da tabbatar da daidaiton ayyukan jam’iyyar kafin zabukan gaba.


Kwamitin zai kuma rika gabatar da rahoton ayyukansa a kowane wata ga Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Yankin Arewa maso Gabas da kuma Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa.


An nada Comrade Paul Ahundana a matsayin shugaban rikon kwarya na jihar, yayin da Hon. Mohammed Abdulrahman zai rike matsayin sakataren jihar. Sauran mambobin sun haɗa da Hon. Salihu Aliyu (mataimakin shugaban jam’iyya), Dakta Zion Maina (sakataren shirye-shirye), Alhaji Saidu Mohammed (ma’ajin kudi), da kuma Mrs. Malia Sanweri (sakatariyar kuɗi).


Jam’iyyar ta bayyana cewa wa’adin kwamitin zai kasance na kwanaki 90 daga ranar da aka fitar da wasikar, sai dai idan kwamitin ƙasa ya yanke wani sabon mataki.


Dakta Agunloye ya taya sabbin shugabannin murna tare da kira gare su da su karanta kundin tsarin mulkin jam’iyyar, su kuma kiyaye manufofin gaskiya da kyakkyawan shugabanci da jam’iyyar ke dogaro da su.


An kuma tura kwafen wasikar nadin zuwa hukumomi kamar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Hukumar Zaɓe ta Jihar Adamawa, Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya, Hukumar Tsaron Farar Hula (NSCDC), da Hukumar Tsaron Cikin Gida (DSS).


Hedikwatar jam’iyyar SDP na ƙasa na da adireshin a lamba 17, titin Nairobi, kusa da Parakou Crescent, Wuse 2, Abuja.


SDP – Domin Ci gaba, Kyakkyawan Shugabanci, da Adalci ga Jama’a.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT