An kaddamar da kwamitin neman Zaben Tinubu Ta Shatima a jahar Taraba.
An kaddamar da fara gangamin neman zabe shugaban kasa Bola Ahmed Tinibu da Shatima a karkashin jam iyar A P C a jahar Taraba.
Ministan sifiri a Najeriya Alhaji Mu azu Sambo Jaji ne ya jagiranci kaddamar da kwamitin da zasuyi aikin nemana zaben Ahmed Bola Tinibu da Shatima a Jalingo fadar gwamnatin jahar Taraba.
Da yake kaddamar da kwamintin Sambo ya kirayesu da suyi aiki tukuru domin hada kan yayan jam iyar ta A P C wanda hakan zai basu damar yin nasara a dukkanin matakai a fadin jahar baki daya.
Ministan yace yana mai farin ciki da Allah ya nuna masa wannan rana na kaddamar da kwamitin da za su jagiranci gangamin neman zabe shugaban a jam iyar A P C wato Bola Tinibu da Shatima.
Ya kuma baiyana cewa Jam iyar A P C jamiya ce da take da manufa mai kyau da kuma gudanar da aikin cigaban kasa. Don haka nema yake kira ga yan Najeriya da su baiwa jam iyar A P C kuria domin ta cigaba da gudanar da aiyukan cigaba da takeyi.
Wasu daga cikin yayan jam iyar ta A P C sun baiyana farin cikin su dangane da wannan taro wanda acewarsu irin wannan taro zai taimaka wajen hadin kan yayan jam iyar ta A P C.
Baya ga ministan wanda shine ko odinaton gangamin neman zaben Tinibu da Shatima a jahar Taraba a kwai yan majalisun dokokin jahar da sanatoci da dai sauransu a matsayin yan kwamitin.
Comments
Post a Comment