An kirayi gwamnatii jahar Adamawa da ta aiwatar da albashi mafi karanci ga ma aikatan kananan hukumomi N L C

An kirayi gwamnatin jahar Adamawa da ta taimaka wajen magance matsalolin daban daban da ma aikatan jahar ke fama dasu a fadin jahar baki daya. Shugaban kungiyar hadakar kwadigo a Najeriya N L C shiyar Jahar Adamawa Kwamuret Emanuel Fashe ne yayi wannan kira a lokacinda yake jawabi a wurin bikin ranan ma aikata na duniya da aka gudanar a dandalin mahmudu ribadau a yola. Kwamuret Emanuel Fashe yace ma aikatan jahar Adamawa na fuskantar matsaloli da dama da suka hada da aiwata da albashin mafi karanci ga ma aikatan kananan hukumomi, da biyan kudin hutu da ma aikatan kebin gwamnati na shekaru 2017, 2018,2019,2020,2021. da inganta fansho na ma aikatan kananan hukumomi, da kuma sanya hanu kan kudirin doka kan ma aikatan kafafen yada labarain jahar ta Adamawa da dai sauransu. Emanuel Fashe ya kuma kirayi gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya debi malamai a makarantu firamare dake kananan hukumomi aahirin da daya dake fadin jahar duba da karancin malamai da aka fama dashi a makarantun. Harwayau ya bukaci da gwamnan ya taimaka ya warware dukkanin bukatun ma aikatan dake fadin jahar domin inganta rayuwarsu da kuma cigaban jahar baki daya. Fashe ya yabawa ma aikatan jahar bisa kokarinsu da kuma hadin kai da suka bayar a lokacin da aka gudanar da zabe wanda a cewarsa hakan ya nuna cewa ma aikatan suna da rawa da zasu iya takawa wajen cigaban jahar dama kasa baki daya. Shima a jawabinsa kwanturola a ma aikata kwadigo ta tarayya Musa Aliyu ya yabawa hadaddiyar kungiyar kwadigo bisa shirya wannan biki a wannan shekara dangane da ranan ma aikata ta duniya. Ya kuma kirayi ma aikatan da sukasance masu hada Kansu domin samun cigaban kungiyar yadda ya kamata a fadin jahar baki daya. Da yake nashi jawabi shugaban kungiyar T U C a jahar Adamawa kwamuret injiniya Dauda Adamu Ali yabawa yayi da yadda aka gudanar da bikin na ranan ma aikatan ta duniya lafiya ba tare da wasu matsaloliba don haka akwai bukatan gwamnati ta taimaka wajen inganta rayuwar ma aikatan dake fadin ta Adamawa baki daya. Shima da yake gabatar da nashi jawabi gwanan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri wanda shugaban ma aikatan gidan gwamnati jahar Adamawa Farfesa Maxwell Gidado ya tabbatarwa ma aikatan cewa gwamnati zatayi iya kokarinta domin ganin an inganta walwalan ma aikatan fadin jahar baki daya. Ya kuma kirayi ma aikatan da sukasance masu baiwa gwamnati hadin kai da goyon baya domin ganin ta cimma burinta na gudanar da aiyukan cigaban jahar baki daya. Kungiyoyin ma aikatu daban daban ne dai suka gudanar da fareti a lokacin bikin da ya gudanar a ranan ma aikatan ta duniya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE