An kirayi maniyata da sukasance masu taka tsantsan da kuma bin doka a lokacin aikin hajji. Suleiman Yusuf.
An kirayi maniyata dake jahar Adamawa da sukasance masu bin dokoki kasar sudiya musammanma a lokacin aikin hajji wanda za a gudanar a wannan shekara domin ganin sun gudanar da aikin hajji karnabbe.
Jami in tsare tsaren aikin hajji karamar hukumar Madagali dake jahar Adamawa Alhaji Suleiman Yusuf ne yayi wannan kira a zantawarsa da jaridar All Nur a yola.
Alhaji Suleiman yace ya kamata kowane maniyaci ya kasance maibin dukkanin ka idodin aikin hajji da kuma dokar kasa mai tsarki wanda acewarsa hakan zaisa maniyaci yayi aikin hajji karbabbe.
Ya kuma shawarci maniyatan da sukasance masu yin taka tsantsan wajen kula da kayakinsu dama jakkunansu domin acewarsa idan sukayi sakaci da jakkunansu wasu zasuyi anfani da wannan damar wajen cutar da su ta sanyamusu wasu kayaki da basu daceba.
Don haka nema yace kada maniyaci ya bari wani yazo ya bashi ajiyar kayakin da bai sansuba ko yace rikemini wannan ina zuwa ko sako don ta haka wani yana iya basu kayakin da hwamnatin Saudiya ba amince da suba.
Saboda haka maniyata su maida hankalin sosai wajen sanya ido da kuma lura da kayakinsu a duk inda suke.
Alhaji Suleiman ya kuma yabawa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa jajircewa da yayi na taimakawa maniyata dama basu dukkanin abinda ya kamata domin ganin sun samu nasaran gudanar da aikin hajji cikin kwanciyar hankali ba tare da matsaloliba.
Jam in tsare tsaren aikin hajji ya kuma rabawa maniyatan karamar hukumar ta Madagali jakkunansu da kayakin sawa na baidaya.
Da yake jawabi a madadin maniyatan Alhaji Dahiru ya nuna jin dadinsa dangane da yadda aka raba musu jakkunan shima godiya yayiwa gwamnan bisa na mijin kokari da yayi na kula da maniyata. dama basu dukkanin abinda suka dace.
Wasu daga cikin maniyatan sun yabawa malamai da suka gabatar musu da bita dangane da aikin hajji tare da yabawa shugabanin hukumar aikin hajji bisa jajirvewa da sukayi wajen ganin maniyatan sun samu dukkanin abunda suka kamata.
Comments
Post a Comment