An yabawa yan jarida dangane da yadda suke gudanar da aiyukansu. Alhaji Adamu.
A yayinda aka gufanar da kinin ranan yancin yan jarida ta duniya an yabawa yan jarida bisa jajircewa da sukeyi a duk lokacinda suke gudanar da aiyukansu.
Alhaji Adamu Jngi wanda aka fi sani da mai hangene yayi wannan kira a zantawarsa da jaridar Al Nur a yola.
Alhaji Adamu Jingi yace yan jarida suna taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin al umma. da kuma ilimantar da al umma baki daya.
Alhaji Adamu yace yan jarida suna nan tamkar tsanine a tsakanin shuwagabanin da takakawa don haka ya zama waji a jinjinawa yan jarida.
Saboda haka nema ya shawarci al umma da sukasance masu baiwa yan jarida hadin kai da goyon baya domin ganin yan jaridan sun samu damar gudanar da aiyukansu.
Alhaji Adamu ya kuma kirayi yan jaridar da sukasance masu gudanar da aiyukansu bil hakki da gaskiya da kuma bin ka idodin aikin jaridan kamar yadda doka ya tanada. Domin samun cigaban aiyukansu yadda ya kamata.
Raman uku ga watan mayu na kowace shekarane dai majalisar dinkin duniya ta aiyana da yazaman Raman yancin yan jarida ta duniya domin dubawa tare da warware matsaloli ko kalubalen da yan jaridan ke fuskanta a duk lokacinda suke gudanar da aiyukansu.
Comments
Post a Comment