Gidauniyar dake yaki da cutar yoyon fitsari a Najeriya ta kudiri aniya kawar da cutar.

An baiyana cewa tsawon nakuda na daya daga cikin abunda ke haddasa cutar yoyon fitsari wanda hakan na jefa uwa da jarirai cikin mawuyacin hali. Shugaban gidauniya fistula a Najeriya Mallam Musa Isa ne ya baiyana haka a lokacinda yake jawabi danhane da ranar yaki da cutar ta yoyon fitsari ta duniya. Mallam Musa Isa yace matsalar samun jinkiri zuwa asibiti da kuma rashin wadatattun cibiyoyin kiwon lafiya musammanma a yankunan karkara suna taimakawa wajen haifar da cutar ta yoyon fitsari. Mallam Isa ya kara da cewa yanayin na talauci da karancin ilimi suma suna taka mahimmiyar rawa wajen musabbabin kamuwa da cutar don haka nema yake kira ga al umma musammanma magidanta da sukasance masu tallafawa matansu a koda yaushe musammanma wadanda ke dauke da juna biyu wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen kaucewa kamuwa da cutar ta yoyon fitsari. Harwayau gidauniyar ta fistula a Najeriya ta gabatar da kautukan yabo ga manyan likitoci da suka taka rawan gani wajen yaki da cutar ta yoyon fitsari, likitocin dai sun hada da Farfesa Kees Waaldijk, Dr Amir Imam Yola, Farfesa Idris Abubakar Suleiman na AKTH da kuma asusun Al umma na majalisar dinkin duniya a wani mataki na ranan yaki da cutar yoyon fitsari ta duniya a wannan shekara ta 2023 wanda akayi a jahar Kano. A yayin bikin ranan yaki da cutar yoyon fitsari ta duniya mata wadanda suka warke daga cutar ta yoyon fitsari akalla dari da sittin da takwas ne sukayi jerin gwano dauke da kwalin da ke neman kawo kasshen matsalar baki daya. Cikin manyan baki da suka halarci bikin da akayi a jahar kano ya samu halartan Kwamishiniyar Ma aikatar harkokin mata na jahar Kano Dr Zahra Muhammed tare da Babban sakatare a ma aikatar da kuma dukkanin mata da direktoci dake ma aikatar kiwon lafiya dana ma aikatar harkokin mata dukkaninsu sun halarci bikin. Majalisar dinkin duniya ta asusu al umma wato UNFPA ta aiyana ranan ashirin da uku na watan biyar na kowace shekara da ya zama ranan yaki da cutar ta yoyon fitsari domin ganin an dakile cutar a duniya baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE