Hukumar aikin hajji jahar Adamawa ta baiyana ranan da za a fara jigilan maniyatan jahar zuwa kasa mai tsarki.
Hukumar aikin hajjin jahar Adamawa tace ta kammala dukkanin shirye shiryenta domin gudanar da aikin hajjin wannan shekara a kasa mai tsarki.
Babban sakataren hukumar a jahar Adamawa Dr Salihu Abubakar ne yabaiyana haka a lokacin da yake jawabi a wurin rufe bita wanda hukumar ta shiryawa maniyata a yola.
Dr Salihu Abubakar yaja hankalin maniyatan da sukasance a shirye domin hukumar ta kammala shirinta na fara tafiya kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajji.
Shugaban hukumar ya kuma sanar da cewa za a fara jigilan maniyatan jahar Adamawa a ranan biyu ga watan shiddan wanan shekara.
Shima a jawabinsa Jami in tsare tsaren aikin hajji karamar hukumar yola ta arewa Alhaji Ya u Gambo ya kirayi maniyatan da sukasance masuyin amfani da abunda suka koya a lokacinda ake yi musu bita domin ganin an samu nasaran gudanar da aikin hajji cikin kwanciyar hankali.
Anashi bangaren Jami in tsare tsaren aikin hajjin karamar hukumar Madagali Alhaji Suleiman Yusuf ya shawarci maniyata da sukasance masu bin doka da oda daga nan Najeriya har zuwa kasa mai tsarki wanda acewarsa bin dokan zai taimaka musu wajen gudanar da aikin hajji yadda ya kamata.
Shima Babban bako a wurin taron Kwamishinan kananan hukumomi da masarautun gargajiya Alhaji Yayaji Minjinyawa ya kirayi maniyatan da sukasance masu neman ilimin kan dukkanin aiyuka domin su samu damar gudanar da aikin hajjinsu cikin lumana.
Wasu daga cikin maniyatan sun baiyana farin cikin dangane da bitan da aka gudanar musu tare da tabbatar dacewa zasuyi amfani da abunda aka koya musu.
Akalla maniyata dubu biyu da dari biyar da saba in da hudu ne dai zasu gudanar da aikin hajji wannan shekara daga jahar Adamawa.
Comments
Post a Comment