Kamfanin Dangote zai cigaba da karfafa dankon zumunci a tsakaninsa da al ummomi dake kewaye dashi.

Kamfanin Dangote ya kara jaddada a niyyar shi na na ci gaba da zaman lafiya da al'ummomi dake kewaye da shi. Babban Manajan kamfanin, Malam Bello Danmusa ne ya baiynana haka yayin zaman ganawa da masu ruwa da tsaki da ya wakana a garin Numan. Babban Manajan kamfanin, Malam Bello Danmusa yace gina kyakkyawan alaka da al'umomi dake kewaye da kamfanin abu ne wanda ya dauka da muhimmanci matuka shi yasa ma ta shirya wannan taron ganawar. Danmusa yace, kamfanin Dangote dake Numan na aiki tare da al'umomin dake kewaye da shi a fannonin ilimi da aiyukan tallafi ta hanyoyi daya tsara domin inganta rayuwan mutanen da ke yankin. A cewar shi, kamfanin Dangote zai ci gaba da ganawa da masu ruwa da tsakin domin yin hakan zai basu daman tattaunawa tare da bullo da hanyoyi da za a amfana, a kuma samu zaman lafiya tsakanin juna domin ci gaban kamfanin, al'ummomin, jaha dama kasa baki daya. Da yayi jawabi kan muhimmancin wannan zama, Babban Jami'in Ofishin hulda da al'umma na kamfanin Dangote dake Numan, Daniel Andrew yave makasudin wannan ganawa da masu ruwa da tsaki da kamfanin da yanke shawaran shiryawa bayan ko wani wata uku shine ci gaba da more kyakkyawar mu'amala da aka kulla tun farko. Yace ganawa da masu ruwa da tsakin zai taimaka matuka musamman gurin musanyar ra'ayoyi tare da bada tabbacin zama tare. Tun farko dai a jawabin shi na bude taron, Daya daga cikin shugabannin kamfanin Suga na Dangote dake Numan, Mista Chinnaya Silvain yace kamfanin Dangote ya yanke shawaran gudanar da wannan taron masu ruwa da tsaki bayan duk wata uku domin karfafa cudanya da mu'amala da al'unmomi dake kewaye da shi, ya kuma baiyana musu irin aiyuka da yake yi domin ganin an samu ci gaba. Ya kirayi duk wadanda suka kasance a zaman da su amfani da daman gurin tattaunawa da jami'an kamfanin kan batutuwa da zasu amfani bangarorin biyu. Hakimin Borrong , Cif Lawsan Gadiel Nayina da ya kasance a taron yace taton na da muhimmanci matuka domin zai taimaka gurin karfafa mu'amala dake tsakanin al'ummomin da kamfanin Dangote. Ya kara da cewa tallafawa mutane dake wannan yanki zai taimaka gurin cimma samun zaman lafiya dama ci gaba.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.