Kamfanin Dangote zaici gaba da taimakawa harkar ilimi a Najeriya.

An kirayi iyaye da su baiwa ilimin yayan su muhimmanci. Babban manajan sashin aiyukan kamfanin dangote dake numan, Alhaji Bello Dan-musa ne yayi wannan kira yayin bukin ranan yara na bana, wanda ya wakana a sashin firamaren makarantan ma'aikatan dangote dake harabar kamfanin a Numan. Babban manajan sashin aiyukan kamfanin dangote, Alhaji Bello Dan- musa yace nasaran karatun duk wani da na da alaka da kokarin iyayen shi. Dan-mua yace Kamfanin dangote zai ci gaba da tallafawa ci gaban ilimi a matakin jaha da na kasa baki daya. Ya kara da cewa kamfanin zai ci gaba da kula da jin dadin malaman makarantan shi kamar yadda ya dace. Shugaban kungiyar malamai da iyaye da malaman makarantan wato PTA, mallam Lawan Adamu yace ware rana na musaman domin bikin ranar yara na da muhimma so sai har ma wa iyaye wadanda ke tallafa wa yaran a kulla yaumin. A cewar shi, koyawa yara sana'oin hannu zai taimaka musu bayan sun manyanta. A nata jawa, shugaban malaman makarantar, misis Grace Ella tace ranar kamar irin wannan na baiwa yara damar cudanya da juna. Misis Grace tace kamar yadda taken bukin na bana na kasa ya tanadar, wato saka karin kudade a ilimin firamare, dama muradin kamfanin dangote da na daurewan harkokin doron kasa, bana za ta yi amfani da damar wajen sarrafa datti zuwa kayan amfanin cikin gida. Wasu daga cikin jerin abubuwa fa suka wakana yayin bikin sun hada da gasar kacici kacici, rawan gargajiya, da dai sauran su.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE