Manoma a jahar Adamawa sunkirayi gwamnatin tarayya da ta taimak musu da inganceccen iri.

Manoma ajahar Adamawa sun kirayi gwamnatin tarayya dana jahar da su taimaka musu da inganceccen iri dama takin zamani domin bunksa harkokin noma harma da samar da wadaceccen abinci a jaha dama kasa baki daya. A hiransu da jarida All nur manoman sukace samarwa manomi inganceccen iri yana da da mutukam muhimmanci ga manomi Wanda hakan zai taimaka wajen Samar amfanin gona mai yawa. Alhaji Muhammed Saleh Gwalan shugaban kungiyar manoma auduga a jahar Adamawa yace dukkanin harkokin noma da manoma zasuyi in basu samu inganceccen iriba to zasu fuskanci matsala a harkokinsu na noma don haka ya zama wajibi su mika kokok baransu ga gwamnatin taryya dana jahar da su agaza musu da wadadattun kayakin noma Wanda hakan zai basu kwarin gwiwar bunkasa harkokin noma a fadin jahar baki daya. Sale gwalan ya kuma kirayi manoma da sukasance masu neman ilimin harkokin noma duba da yanzu harkokin noman na kokarin komawa na zani wato a kimiyance. Saboda haka manoma su tashi tsaye wajen neman sanin yadda zasu inganta harkokin nomansu. Ya kuma shawarci manoma musammanma masu girbe amfanin gonansu na rani da kada suyi saurin sayar da kayakin da suka noma domin kaucewa shiga wani yanayi na matsalar tsadar kayakin noma duk da cewa an fuskanci lokacin damina. Shima malam Sani manomine a bogare yace dolenefa gwamnati dama masu ruwa da tsakai akan harkokin noma sun taimakawa manoma Wanda hakan zai baiwa manoman damar gudanar da aiyukansu yadda ya kamata

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE