Matasa da mata sama da dubu hudu ne zasu amfana da shirin koyon sana o i daban daban a jahar Adamawa.

An kirayi matasa dama mata dake fadin jahar Adamawa da su maida hankali wajen koyon sanana o i da zasu dogra da Kansu domin ganin sun kare martabansu dama cigaban all umma baki daya. Shugabar hukumar rage radadin talauci da samar da aikinyi na jahar Adamawa wato PAWECA Hajiya Aishatu Bawa Bello ce tayi wannan kira a jin kadan da duba yadda ake horas da matasa da mata kan sana o i daban daban a jahar Adamawa. Hajiya Aishatu Bawa tace gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yana iya kokarinsa na ganin cewa matasa da mata dake fadin jahar sun samu sana o in dogaro da kai Wanda avewarta hakan zai taimaka wajen samar da zamam lafiya dama bunkasa tattalin Arzikin jahar dama kasa baki daya. Hajiya Aishatu tace ada ana biyansu lawus nasu akan dubu biyar to Amman gwamna ya kara musu zuwa dubu goma a kowane watan don haka nema ya shawarci matasan da su maida hankali sosai wajen koyon sana o i. Shima a jawabinsa Kwamishinan ma aikatan koyar da sana o i da samar da aikinyi a jahar Adamawa Mr James Iliya ya kirayi matasan da su sani koyon sana ar dogaro da kai yana da mutukan muhimmanci domin zasu samu damar gudanar da bukatunsu cikin kwanciya hankali ba tare da wasu matsaloliba. Ya kuma baiyana cewa za a horar da matasa sana o i da suka hada da aiki tela, harkokin noma, da kai sauransu. Wasu daga cikin wadanda za a horar din dai sun baiyana farin cikinsu dangane da wannan horo da za ayi musu kuma zasuyi amfani da abund aka koya musu ta banyan da ta dace domin samun cigaban al ummarsu baki daya. Akalla matasa da mata sama da dubu hudu ne dai wadanda suka fito daga kananan hukumomi ashirin da daya ne dai zasu amfana da gajiyar shirin a cibiyoyi goma dake fadin jahar Adamawa.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.