Mazauna yankin geriyo sun bukaci da gwamnati ta taimaka musu.
Mazauna yankin geriyo sun kirayi hwamnatin tarayya dana jahar harma dana kananan hukumomi da su taimaka musu da makaranta, da cibiyar kiwon lafiya a yankin domin yaransu su samu inganceccen ilimi.
A hiransa da jaridar Al nur Malam Muhammed Na taala Ibrahim Wanda kuma shinema farkon zama a yankin yace sun kwashe akalla shekaru saba in suna zaune ba tare da makaranta ko wata cibiyar kiwon lafiyaba. Don haknema ya zama wajibi su kirayi gwamnatin tarayya dana jahar dana kananan hukumomi harm da kungiyoyi masu zamnan Kansu da su taimaka musu domin ganin yaransu sun samu ilimi yadda ya kamata.
Mazuna yankin na geriyo dai akasarinsu masuntane kuma suna zaune ne a daf da bakin tafkin geriyo dake unguwar jambutu a cikin karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Comments
Post a Comment