Rudunan yan sanda a jahar Adamawa tasha alwashin ceto mutanen da wasu sukayi garkuwa da su a jahar.
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta baza komarta domin ceto tare da zaukulo wadanda sukayi garkuwa da rev.Mike Ochigbo da pastor John Moses a fadin jahar baki daya.
Rundunan ta baiyana hakane a wata sanarwa da ta fitar ta hanun kakakinta SP Suleiman Yahay Nguroje wanda kuma aka rabawa manema labarai a yola.
Sanarwan tace dagajin labarin cewa anyi garkuwa da mutanen biyu sai kwamishinan yan sandan jahar ta Adamawa Afolabi Babatola ya bada umurnin tura jami an tsaro domin shiga sako sako dama lunguna domin ganin an kama wadanda sukayi garkuwa da mutanen biyu harma da duk wanda yake da hanu ayin garkuwa da mutanen biyu.
Sanarwa ta kuma kara da cewa kwamishin ya umurci dukkanin manyan jami an yan sandan dake fadin jahar da su dukufa wajen sanya ido domin ganin an samu nasaran cika hanu da wadanda sukayi garkuwa da mutanen.
Kwamishin ya kuma tabbatarwa da cewa rundunan a shirye take ta kare rayuka da dukiyoyin al umma saboda haka rundunan na bukatan hadin kai da goyon baya daga al umma musammanma yan siyasa da su shawarci magoya bayansu da su kaucewa duk abunda zai kawo tashin hankali a tsakanin al umma, domin samar da zaman lafiya mai daurewa.
Kuma rundunan a shirye take ta kwato mutanen da akayi garkuwa da su cikin koshin lafiya tare da kiran jama a da su kasance masu kai rahoton dukkanin abinda basu amince da shiba zuwa ofishin yan sanda mafi kusa da su.
Harwayau rundunan ta bada numbobin yawa domin kira na gaggawa kamar haka 08089671313
08130013347
Comments
Post a Comment