Rundunan soji na operation hadin kai ta ceto yaran matan chibok biyu daga dajin sambisa a jahar Borno.

Rundunan operation Hadin kai a jahar Borno ta ceto yaran mata biyu yan chibok ciki harda wanda ta haifu kwanan nan gwamnatin jahar zata mikasu ga iyalensu bayan an duba lafiyarsu. Da yake gabatarwa manema labarai yaran mata a shelkwatan rundunan operation Hadin kai a jahar Borno major janar Ibrahim Ali yece a ranan 21-4-2023 ne suka ceto yaran daga dajin Sambisa a jahar ta Borno. Yaran mata biyun dai sun hada da Esther Marcus yar shekaru 26 da haifuwa sai Hauwa Maltha itama yar shekaru 26 da haifuwa. A cewar Hauwa Maltha an cetota tana dauke da cikin wata takwas da sati biyu kuma ta haifi da na miji a ran 28-4-2023 a asibitin rundunan sojojin na bakwai. Rundunan ta baiyana cewa Hauwa Maltha ta auri yan boko haram daban daban har uku kuma dukkaninsu sun gamu da ajalinsu biyo bayan tafo mugama da sukayi da sojiji a tafkin chadi da kuma dajin Sambisa. Ita kuwa Esther Marcus tilastata akayi ta auri mayakin na boko haram wanda aka sani da suna Garus wanda shima an kasheshi awni musayan wuta da akayi da rundunan daga bisani kuma ta auri wani mai suna Abba dake Ukuba. Kwamandan rundunan Major Janar Ibrahim Ali ya tabbatarwa al umma yankin arewa masau gabasa da sukwantar da hankalinsu saboda rundunan a shirye take ta kawar da duk wani ta addanci da ma aikata laifuka a yankin baki daya. Yaran mata sun baiyana farin cikinsu dangane da ceto su da akayi daga hanun mayakan na boko haram.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE