Rundunan yan sanda. a jahar Adamawa ta kama magidanci da matarsa bisa zarginsu da cin zarafin maraya.
Rundunan yan sandan jahar Adamawa tana tsare da wani magidanci da matarsa bisa zarginsu da cin zarafin wani maraya dan shekaru sha Daya da haifuwa Mai suna Fahad Abdulkarim Wanda yake karkashin kulawarsu bayan mutuwar mahaifinsa.
Kakakin rundunan yan sandan jahar ta Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yola Kuma aka rabawa manema labarai a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Sanarwa tace magidanci Kamal Idris dan shekaru ashirin da hudu da haifuwa da matarsa Ambasiya Idris yar shekaru sha tara da haifuwa dukkaninsu suna zaune ne a cikin anguwar Wuro Jabbe a cikin karamar hukumar yola ta kudu dake jahar Adamawa. Wadanda ake zarginsu da cin zarafin maraya ta raunatashi.
Rundunan ta samu rahoton sirrine Wanda Kuma hakan yasa rundunan batayi da wasaba wajen daukan mataki Wanda a yanzu hakama yaron Yana asibiti inda yake jinya.
Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya tabbatar da cewa dazaran an kammala bincike kan wadanda ake zargin za a gurfanar dasu gaban kotu domin su fuskanci shariya.
Kwamishinan Yan sandan ya Kuma kirayi daukacin Al ummar jahar Adamawa da sucigaba da taimakawa rundunan yan sandan da dukkanin baiyanai da basu amice da suba domin daukan mataki Akai.
Comments
Post a Comment