Rundunan yan sandan jahar Adamawa tayi Babban kamu.
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta kama wasu mutane biyu wadanda suna ciki wadanda suka gudu daga gidan gyara halinka dake Kuje a Abuja.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar wanda kuma aka ranawa manema labarai a yola.
Mutanen dai sune Atiku Ibrahim mai shakaru talatin da bakwai da haifuwa sai Adamu Ibrahim mai shekaru Arba in da haifuwa wadanda sun gudu daga gidan gyara halinkan ne biyo bayan hari da aka kai a gidan yarin na kuje a Raman 5-6-22. Wanda yayi sanadiyar mazauna gidan yarin akalla dari biyar suka gudu.
Kuma ana tsare da sune bisa zarginsu da satan shanu dama sauran lafuka Wanda kuma suna zaune a gidan yarin ne tundaga shekara ta 2021.biyo bayan zarginsu da safaran makamai kuma su tabbatarwa rundunan jahar Adamawa cewa suna cikin wadanda suka gudu daga gidan yarin kuje.
Kuma sun baiyana cewa sunama zaman jiran shariya ne a gidan yarin bisa zarginsu da safaran makamai.
Kawo yan zu dai kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya bada umurni da a gaggauta mikasu ga hukumar dake kula da gidajen gyara halinka dake jahar Adamawa domin daukan matakin da ya dace.
Comments
Post a Comment