Sabon kwamandan Civil Defenve a jahar Adamawa ya fara aiki.
Sabon kwamandan Rundunan tsaron bada kariya ga farin kaya.wato Civil defence a Najeriya shiyar jahar Adamawa ya karbi ragamar mulkin rundunan a jahar Adamawa.
Jami in watsa labarain rundunan a jahar Adamawa SC Dimas Yakubu Bille ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yola wanda aka rabawa manema labarai.
Sanarwan tayi nuna cewa kwamandan rundunan mai barin gado Muhammed Sanusi Bello ya mikawa Sabon kwamandan Ibrahim Mainasara ragamar mulkin rundunan a shelkwatar rundunan dake sakatariyar tarayya dake nan yola.
Da yake jawabi kwamanda maibarin gado ya kirayi Jami an rundunan da sukasance masu baiwa Sabon kwamandan hadin kai da goyon baya a koda yaushe domin ganin an samu inganci tsaro a fadin jaha baki daya.ya kuma yabawa Jami an bisa jajircewarsu na ganin an samar da zaman lafiya a fadin jahar.
Shima a jawabisa sabon kwamandan Ibrahim Mainasara yayi Alkawarin yin aiki kafada da kafada da Jami an rundunan domin samun cigaba da ma wanzar da zaman lafiya a tsakanin al umma dake fadin jahar.
Ya kuma tabbatarwa gwamnatin jahar Adamawa dama al ummar jahar cewa rundunan a shirye take ta kare rayuka dama dukiyiyim Jama a.
Don haka nema yake kira ga al ummar jahar da su kasance masu baiwa rundunan hadin kai da goyon baya domin ganin rundunan da samu nasaran dakile aiyukan ta addanci a fadin jahar ta Adamawa baki daya.
Comments
Post a Comment