An shiryawa mata yan Jarida horo na kwanaki uku a yola.

Daga Ibrahim Abubakar yola
Wata kungiya maizaman kanta mai gudanar da aiyukan cigaba OISD ta kaddamar da fara horas da mata yan jaridu a wani mataki na inganta aiyukan mata a kafafen yada labarai. An dai kadamar da horon ne a Jami ar Amurka dake Najeriya dake nan yola wato AUN mai taken zata iya. Mata yan jarida wadanda aka zakulosu daga ahiyar arewa masaugabas domin ganin an samu daidaito da kuma inganta aiyukan aikin jarida ga mata. A jawabinsa Babban darekta kungiyar Mr Jamilu Yusuf ya baiyana cewa ana gudanar da wannan horanne tare da hadin gwiwar sashin harkokin yada labarain ofishin jakadançi Amurka dake Abuja. Jamilu Yusuf yace sun dauki matakin hakane domin karawa matan kwarin gwiwa cigaba da aiyukansu na jarida yadda yakamata. Shima a naahi bangaren shugaban sashin harkokin yada labarai na ofiahin jakadancin Amurka dake Abuja Mr Robert Gabor ya baiyana cewa ofishin jakadancin na Amurka a shirye take domin ganin an samu nasaran bunkasa harkokin aikin jarida ga mata a wani mataki na samun daidaito. Yace horas da mata zai taimaka wajen bunkasa tare da cigaban aikin jarida da kuma ganin matan saun samu damar bada tasu gudumawa.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.