Rundunan yan sandan Najeriya ta bugi kirjin inganta tsaro a fadin kasa baki Daya.
yan sandan Najeriya tasha alwashin inganta tsaro a fadin kasar domin dakile aiyukan ta addanci a wani mataki na maido da zaman lafiya a dukkanin sassan Najeriya.
Babban aifeton yan sandan Najeriya Kayode Adeolu Edbetokun ne ya baiyana haka a lokcinda ya jagoranci wani taro da rundunan ta gudanar da manyan Jami an yan sandan da suka hada mataimakan Babban sifeton yan sandan, da kwamishinoni, dama kwamandodi daban daban dangane da mataki da ya kamata a dauka domin magance matsalar tsaro da ake fama dashi.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunan yan sandan na kasa ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar ta baiyana cewa taron ya hada dukkanin masu ruwa da tsaki domin tattaunawa da kima zakulo hanyoyin samun nasaran takawa ta addanci birki.
Da yake jawabi dangane da zaben gwamnonin jihohin Bayelsa, Imo, Kogi, dake tafe yace an dauki dukkanin matakai da suka dace domin ganin an samu nasaran gudanar da zaben cikin tsanaki ba tare da fargababa domin acewarsa rundunan bazatayi da wasaba wajen girke Jami anta domin tabbatar da tsaro a lokacin zabukan, don haka akwai bukata hada kai da kuma yin aiki tare da masu ruwa da tsaki wanda haka zai taimaka wajen cimma nasaran.
Da wannan ne yake kira ga al umma da sucigaba da baiwa rundunan hadin kai da goyon baya da kuma taimaka musu da wasu bayanain sirri da zai basu damar wanzar da zaman lafiya a tsakanin Jama a.
A yayin gudanar da taron ne aka karawa Bello Makwashi makamin mataimakin Babban sifeton yan sanda wato DIG. Bayan tayashi murnan Babban sifeton yan sandan ya kirayeshi da ya gudanar da aiyukansa yadda ya kamata bisa tsarin doka domin samun cigaban rundunan dama kasa baki daya.
Comments
Post a Comment