An yabawa Yan jaridan gidan gwamnati bisa kokarin su na fadakar da Al umma dangane da aiyukan gwamnatin jahar.

Gwamnan jahar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya baiyana godiyar shi wa yan jarida da masu harkar yada labarai na jahar bisa gudummawar da suke bayarwa gurin kare danokradiya a jahar. Governor Ahmadu Umaru Fintiri ya yi wannan godiya ne yayin wani buki na musamman da akayi wa lakabi da bukin nasara , wanda aka shirya wa yan jarida musamman wadanda suke aiki a gidan gwamnati a hutun karshen mako, da suka kasance da gwamnan tun wa' adi na farko har zuwa yanzu. Governor Ahmadu Umaru Fintiri, wanda ya samu wakilcin shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, Dakta Edgar Emos Sunday yayin bikin ba za a iya misalta irin gudunmawar da yan jarida ke bayar wa a jahar ba, musamman wadanda suka gudanar da aiyukan su a gidan gwamnati , wannan ne ya sa aka shirya wannan buki domin jinjina musu gurin kokarin daidai ta harkokin danokradiya a jahar. Governor Ahmadu Umaru Fintiri yace gwamnatin shi na matukar daukan yan jarida da muhimmanci a jahar. A cewar gwamnatin, bukin har wa yau na danokradiya dama al'ummar jahar ne wadanda suka yi tsayuwar daka domin baiyana ra'ayoyin su na baiwa gwamnatin shi tafiyar da harkokin jahar ta hanyar zaben shi Gwamnan jahar domin ci gaban ta. Ya kuma godewa wadanda suka shirya bukin tare da bada tabbacin biyar gwamnatin shi ciyar da jahar Adamawa gaba. A sakonnin su na fatan alkharir, komishinan harkokin kananan hukumomi , Yayaji Mijinyawa, da komishinan ilimi Dr Umar Garba pella, da kuma komishiniyar yada labarai da tsare tsare , Neido Geoffrey Kufulto, da sakataren din din din na ma'aikatar yada labarai da tsare tsare Mr Solomon kumangar, da mai bada shawara na musamman kan yada labarai da tsare-tsare Dr John Ngamsa duk sun mika godiya ga yan jarida gidan gwamnati bisa kokarin su na kasancewa da gwamnan, ba dare ba ranan, musamman lokacin kamfen, wadanda gudunmawar su abun yabawa ne matuka. Tun farko dai, jagoran bukin kuma sakataren yada labarai na gwamnan jaha, Humwashi Wonosikou yace makasudin shirya wannan buki dai shine a godewa yan jarida dake gidan gwamnati, a kuma yi cudanya , a ci a sha tare da su. Mr Humwashi Wonosikou ya kara da cewa gwamnatin jahar da ma daukacin al'ummar ta baki daya suna yaba da kokarin wadannan yan jarida gurin fadakar da al'umma irin tsare tsaren gwamnati da Fintiri ke jagoranta dama yadda za su ci moriyar su. Yayin bikin na musamman dai, yan jaridan sun tattauna da juna, dama shugabannin nasu, yayin da suka ci suka kuma sha.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.