Babban Hafsan tsaron Najeriya ya gana da Babban sifeton yan sandan Najeriya.

A wani mataki na inganta tsaro da kuma hadin gwiwa a tsakanin hukumomin tsaro, Babban Hafsan tsaron Najeriya janaral Christopha Gwabin Musa tare da manyan Jami an soji sun ziyarci Babban sifeton yan sandan Najeriya a ofishinsa dake shelkwatar rundunan a Abuja domin kara karfafa halaka da kuma hada kai wajen yin aiki tare a tsakanin yan sandan da sojoji domin kare kasa daga matsalar tsaro. Kakakin rundunan yan sandan na kasa ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar wanda kuma aka rabawa manema labarai a Abuja. Babban Hafsan tsaron ya taya Babban sifeton yan sandan murnan tabbatar da nadinsa a matsayin Babban sifeton yan sandan Najeriya tare yaba masa bisa kokarinsa na tura rundunan yan sandan kwantar da tarzoma domin dakile aiyukan masu tada kayan baya. Tare kuma da nuna alhininsa da harin da wasu sojoji suka kai a shelkwatan rundunan yan sandan dake yola a jahar Adamawa. Ya kuma tabbatar da cewa za agudanar da bincike dangane da lamarin, don haka nema yake kira ga hukumomin tsaron da sukasance masu da a da kuma hada kansu waje guda domin yin aiki kafada da kafada domin ganin an kawo ga karshen aikata laifuka a fadin Najeriya baki daya. Shima anshi bangaren Babban sifeton yan sandan Kayode Adeolu ya taya Babban Hafsan murnan bashi mukamin Babban Hafsan tsaro da akayi tare da tabbatar masa cewa rundunan yan sandan Najeriya a ahirye take taci gaba da kyakkyawar halaka a tsakanin dukkanin hukumomin tsaro , ya kuma nuna gamsuwarsa da yadda za a gudanar da bincike kan abinda ya faru a jahar Adamawa taren da yin fatan lamarin bazai sake faruwaba. A daya hanun kuma Babban sifeton ya karbi ziyaran minister ma aikatar harkokin mata a Najeriya Barista Uju Kennedy Ohaneye ita da gawagarta da kuma Babban darektan hukumar hana fataucin biladam wato NAPTIP farfesa Fatima Waziri inda suka tattauna batutuwa da dama ciki harda batun kan iyakokin Najeriya da dai sauransu. Babban sifeton ya tabbatarwa ministan cewa rundunan zata hada kai da ma aikatar domin samun cigaba da ma inganta tsaro a kan iyakokin. Domin ganin an dakile safaran biladama dama sauran aikata laifuka baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.