Babban sifeton yan sanda Najeriya ya jadda da aniyar rundunan na cigaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro wajen kare rayuka dama dukiyoyin Al umma.
Biyo bayan rikici da aka samu kwanan nan a tsakanin yan sanda da sojoji lamarinda yayi sanadiyar mutuwar wani isfeto wato Daniel Jacob. Babban sfeton yan sandan Najeriya Kayode Adeolu Egbetokun ya kawo ziyara jahar Adamawa a wani mataki na jajjantawa dangane da mutuwar Jami in dan sandan.
A jawabinsa da ya gudanar a wurin taron jamin an yan sandan da aka gudanar a shelkwatar rundunan yan sandan a jahar Adamawa Babban sifeton yan sandan ya nuna damuwarsa dangane da aukuwar lamarin tare da yin fatan lamarin maikama da wannan ba zai sake faruwa ba a fadin Najeriya.
Babban sifeton ya kuma jaddada aniyar rundunan na cigaba da hada kai da sojojin dama sauran hukumomin tsaro domin ganin an karewa rayuka da ma dukiyoyin al umma baki daya.
Ya kuma yabawa rundunan yan sandan jahar Adamawa bisa sadaukar da kai da sukeyi wajen gudanar da aiyukansu yadda ya kamata domin kare al umma dake fadin jahar.
Harwayau ya kuma yabawa kwamitinnan dake taimakawa rundunan yan sanda wato PCRC da yan banga dama Mafarauta bisa irin gudumawa da suke nayarwa wajen dakile aiyukan masu tada kayan baya.
Babban sifeton ya kuma kirayi al umma da sukasance suna baiwa rundunan yan sandan hadinkai da goyon baya domin ganin rundunan ta samu nasara wajen kare rayuka dama dukiyoyin al umma baki daya.
A jawabinsa shugaban kwamitin na PCRC a jahar Adamawa Mr Attah Mustafa ya baiyana alhininsa dangane da ta kaddama da ta shiga tsakanin sojojin da yan sanda harma yakai da rasa Jami in dan sanda, sboda hakanema a madadaim kwamitin sun taimakawa iyalen marigayin da kayakin abinci da suka hada da buhun shinkafa, galon na mai da dai, da kudi dubu dari da dai sauranasu.
Shima a nashi bangaren sugaban kungiyar kare yanci yan jahar Adamawa Alhaji Hussaini Gambo Bello na Kura yabawa yayiwa Babban sifeton yan sandan bisa ziyara da ya kawawowa jahar ta Adamawa. Shima ya nuna takaicinsa dangane da matsala da aka samu a tsakanin yan sanda da sojoji, tare da kiran hukumomin tsaron biyu da sukasance masu kai zuciya nesa domin kaucewa sake aukuwar lamarin.
Comments
Post a Comment