Babban sifeton yan sandan Najeriya ya yabawa hukumomin tsaro.
Babban sifeton yan sandan Najeriya Kayode Adeolu Egbetokun ya yabawa dukkanin Jami an yan sandan Najeriya dama sauran hukumomin tsaro bisa rawan da suka taka wajen inganta tsaro a lokacin zabe gwamnonin da aka gudanar a jihohin Bayelsa, Imo da Kuna jahar Kogi.
Kakakin rundunan yan sandan ta kasa ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja
Sanarwan ta baiyana cewa Babban sifeton Yan sandan yace Jami an Yan sandan dama sauran hukumomin tsaro sun yaka rawan gani wajen bata tsaro Dama kariya a lokacinda ake gudanar da zabukan.
Babban sifeton yace zaben da ya gudana a jihohin uku ingancaccen zabe ne Wanda Kuma hakan ya biyo bayan tsayin daka da jami an tsaro aukayi wajen kare masu kada kuri a domin tabbatar da cewa sunyi zabe cikin kaunciyar hankali ba tare da matsalaba.
A Daya hanun Kuma dangane da matsàloli da suka faru a lokacin zaben kuwa tunin Babban sifeton Yan sandan ya bada umurnin ga Babban Jami in dake kula da harkokin zabe karkashin mataimakin Babban sifeton Yan sanda Wanda ke sashin bincike mayan lafuka da ya gaggauta fara bincike dangane da lamarin.
Babban sifeton ya Kuma baiyana Jin dadinsa dangane da yadda hukumomin tsaro suka bada hadin Kai da goyon baya domin ganin zabukan sun gudana cikin tsanaki.ya Kuma kirayi Jami an tsaron da su cigaba da irin wannan na mijin kokari da sukeyi domin gudanar da aiyukansu bisa kwarewa a wani mataki na kare martabar dimokiradiya a fadin Najeriya baki Daya.
Comments
Post a Comment