Babban sifeton Yan sandan Najeriya ya ziyarci jahar Adamawa

.
Babban sifeton yan sandan Najeriya Kayode Adeolu Egbetokun ya ziyarci jahar Adamawa domin jajantawa da nuna alhinisa dangane rikici da ya shiga tsakanin sojoji da yan sanda a kwanan nan lamarinda yayi sanadiyar mutuwar Jami in Dan sanda Daya wato isfeta Daniel Jacob. .Kayode Adeolu ya kuma gana da masuruwa da tsaki da suka hada da gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri da Mai martabar Lamidon Adamawa Dr Barkindo Aliyu Mustafa. Kakakin rundunan yan sandan a Najeriya ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja A yayin ziyaran Babban sifeton yane hadin kai a tsakanin rundunan yan sandan da gwamnatin jahar jarma da sarakunan gargajiya dake fadin jahar a wani mataki na inganta tsaro domin magance matsalar tsaro da suka addabi jama a.
Babban sifeton ya Kuma tattauna da Jami an rundunan a jahar Adamawa karkashin jagorancin kwamishinan Yan sandan jahar Afolabi Babatola. Ya Kuma yabawa Jami an Yan sandan bisa na mijin kokari da sukeyi wajen gudanar da aiyukansu don haka a shirye yake ya cigaba da basu goyon baya a Koda yaushe a duk lokacinda suke gudanar da aiyukansu domin ganin anbi doka da oda. Ya Kuma baiyana irin muhimmancin da ke da akwai na hadin Kai a tsakanin Yan sandan dama sauran hukumomin tsaro domin acewarsu rundunan yan sandan bata fada da sauran hukumomin tsaro, ya Kuma tabbatar da cewa za a inganta walwalal Jami an dama basu horo. Ciki wadanda suka marawa Babban sifeton Yan sandan baya wajen Kai ziyaran dai sun hada DIG Bala Ciroma da DIG Ede Ayuba Ekpeji sai AIG Danladi Lalas sai Kuma kakakin rundunan ta kasa ACP Olumuyiwa Adejobi. Harwayau Babban sifeton ya nuna damuwarsa dangane da aukuwar lamarin, inda ya jajinyawa iyalen maragayi tare da tabbatar musu cewa za a gudanar da adalci dangane da lamarin, tare da yabawa suhugaban PCRC Dana kungiyar tajin kare hakkin Yan jahar Adamawa wato ACCA da mafarauta bisa irin taimakawa da sukeyi wa rundunan yan sandan dama taiamako da sukayiwa iyalen marigayin. Babban sifeton ya Kuma godewa gwamnan jahar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri da Lamidon Adamawa Dr Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa dama Al umma jahar Adamawa bisa kokarinsu na taimakawa rundunan. Ya Kuma tabbatar da cewa rundunan yan sandan zataci gaba da hada Kai da gwamnatin jahar da sarakunan gargajiya domin gaggauta Samar da zaman lafiya Mai daurewa a fadin jahar baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.