Gidauniyar Attarahum ta rarraba kayakin abinci wa mutane Sama da arba in a jahar Adamawa.
Gidauniyar Attarahum ta rarraba kayakin abinci wa marassa galihu sama da arba in a jahar Adamawa domin su samu sauki rayuwa duba da yanayi da ake ciki na matsalar rayuwa.
Da yake jawabi a lokacin rarraba kayakin shugaban Gidauniyar Attarahum a jahar Adamawa Mllam Mukhtar Dayyib yace sun dauki matakin hakane domin ragewa Al umma radadin wahalar rayuwa da ake ciki a halin yanzu.
Mallam Mukhtar Dayyib yace daman manufofin Gidauniyar shine taimakawa gajiyayyu, da marayu, Kuma basu yakaita ga musulmai kawaiba harma da mabiya addinin kirista ma suna taimaka musu.
Mallam Dayyib ya Kara da cewa kawo yanzu Gidauniyar tana da rassa a dukkanin kananan hukumomi ashirin da Daya dake fadin jahar ta Adamawa. Kuma sun dauki matakin Bude rassanne domin fadada aiyukansu na taimakawa Al umma.
Ya Kuma kirayi gwamnatin tarayya Dana jahar da sukasance suna taimakawa mabukata a Koda yaushe domin kowa nasune, saboda haka ana cikin wani yanayi a yanzu na matsalar rayuwa.
Shima anashi jawabi sakataren Gidauniyar a jahar Adamawa Mallam Mamman Nasir yace Gidauniyar tazo da abinda take dashi domin tallafawa mabukata domin Suma su rage radadin wahala da ake ciki a yanzu.
Wasu daga cikin wadanda suka samu tallafi sun baiyana godiyarsu da Jin dadinsa bisa taimakon da suka samu daga Gidauniyar ta Attarahum domin acewarsu wannan zaiyaimaka musu wajen rage radadin wahalar rayuwa da ake ciki.
Sun Kuma kirayi sauran kungiyoyi da suyi koyi da irin wannan taimako da Gidauniyar Attarahum tayi Wanda hakan zai taimaka wajen hadin Kai dama zaman lafiya.
kayakin da abinci da aka rarraban dai sun hada da shinkafa taliya da dai sauransu.
Comments
Post a Comment