Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa yace jahar tana murmurewa sakamokok rikicin Boko haram.

Gwamnan Jahar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri yace jahar na kan farfadowa daga illar hare haren yan ta’adda a yankin na arewa maso gabas. Gwamnan Ahmadum Umaru Fintiri ya baiyana haka ne yayin da ya karbi bakoncin mambobin hukumar ci gaban yankin arewa maso gabas da aka sake nadawa a lokacin da suka kawo ziyara a ofishin shi cikin aikan su na zaiyar duba aiyuka a yankin na arewa maso gabas. Gwamnan Ahmadu Umaru Fintiri yace har yanzu akwai wasu kanana hukumomi da hanyoyi da gadajen su na bace sakamakon hare haren yan ta’adda. Gwamnan ya kuma koka da dabi’un yan kwangila da suka gaza aiwatar da aiyukan su a jahar bayan amincewa ta kwangilar, wanda acewar shi hakan ya taimaka gurin jefa mutane cikin mawuyacin hali. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya gode wa tawagar da wannan ziyara tare jinjina wa hukumar da irin aiyukan ci gaba da take aiwatarwa musamman a jahar ta Adamawa. Tun farko dai, shugaban hukumar ci gaban yankin arewa maso gabas, manjo Janar Paul Tarfa yace mambobin gudanarwan hukumar sun iso gidan gwamnatin ne domin sake gabatar da kan su, su kuma tabbatar mishi cewa hukumar zata ci gaba gudanar da aiyukan ta kamar yadda ta faro shekaru hudu da suka gabata. Manjo Janar Tarfa ya kuma taya gwamnan murnar nasarar shi a kotun sauraron koken zabuka, ya kuma yaba mishi da a kokarin shi gudanar da aiyukan ci gaba a jahar. Shugaban hukumar yace daga cikin hakkoki da suka rayata a wuyan hukumar shine na hada kai da jahohin dake yankin domin sake gina yankin na arewa maso gabas, wanda hare haren yar ta’adda ya daidaita. Yayin ziyara dai, hukumar ci gaban yankin arewa maso gabas ta baiwa kananan hukumomin jahar su ashirin da hudu na’uririn isar da sakonni wato public address system da kuma takarda dake kunshe da bayanan aiyukan da hukumar ta aiwatar a shekaru hudu da suka gabata.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.