Gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri yace gwamnatinsa na samun goyon baya daga kungiyoyi dake fadin jahar.

Gwamnan jahar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri yace gwamnatin shi na baiwa goyon bayan da take samu daga kungiyoyi da ke fadin jahar muhimmanci musamman irin kungiyar mabiya addinin krista na CAN domin ci gaban jahar. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya baiyana haka ne yayin da ya karbi bakoncin jagororin kungiyar mabiya addinin krista, CAN karkashin jagorancin shugaban ta, Rabaren Dami Mamza wadanda suka zo gidan gwamnati ziyara. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya bada tabbacin cewa yan jahar za su yi urmushi ganin gwamnati na aiyukan saita lamarori da zasu tabbatar da inganta rayuwan su. Gwamnan yace labara na sauyawa a dukkan fannoni dake jahar, musamman a bangarorin ilimi da tsaro ganin a yanzu jahar nan a biyu a jarrabawan kammala sakadandare na NECO da WAEC, kuma ana ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jahar, sabannin yaddaa lamarin ke nan shekaru hudu da rabi, lokacin da gwamnatin shi ta dare karagar mulki. Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin shin a da yakinin inganta rayuwan al’ummar ta ta hanyoyi daban daban. Yayin da yake kara jaddada cewa tafiyar da harkokin jahar ne a gaban gwamnati yanzu, gwamnan ya gode musu da wannan ziyara tare da alwashin aiwatar da Karin aiyukan ci gaban jahar ta Adamawa. Shugaban kungiyar ta CAN, Rabaren Dami Manza yace tawagar ta zo gidan gwamnati ne domin taya gwamnan murnan nasarorin shina cin zaben gwamnan jahar da da kuma wanda ya samu a kotun sauraron karakin zabe. Yace kungiyar na mishi addu’ar nasara kuma zata ci gaba da yin fiye da haka. A wani makamancin haka kuwa, gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa ya gana da jagorancin kungiyar PENTACOSTAL FELLOWSHIP OF NIGERIA, karkashin jagorancin shugaban ta na jaha, Arch Bishop Japhet Tombwaso wadanda suka iso gidan gwamnatin domin suma su taya shi murnan lashe zabe da ma na nasarar kotun sauraron karakin zabe. Gwamnan Fintri ya tabbatar wa tawagar cewa gwamnatin shi zata ci gaba da gudanar da aiyuka babu kama hannun yaro wa al’ummar jahar Adamawa da kuma zaman lafiya tsakanin juna, ya kira su da su ci gaba da addu’oi da baiwa gwamnati goyon baya yayin da take ci gaba da hada kwararru masu hazaka domin ci gaban jahar. Bayan gode musu da wannan ziyara, gwamnan yace gwamnatin shi zata ci gaba da samar wa al’umma tsaro. Tun farko dai, shugaban kingiyar, Arch Bishop Japhet Tombwaso yace sun iso ne domin taya gwamnan murnan nasaran zabe da kuma gode mishi da yadda yake yafiya tare da mabiya addinin krista a jahar. Ya kuma baiyana nasarar gwamnan a matsayin wani lamari daga Allah tare da addu’ar kariya daga Allah yayin da gwamnan ya dau ragamar tafiyar da harkokin jahar.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.