Gwamnan jahar Adamawa ya tattauna da sojoji da yan sanda biyo bayan rashin jituwa da aka samu a tsakaninsu.

Biyo bayan rikici da aka samu a tsakanin sojoji da yan sandan a jahar Adamawa. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa ya gudanar da taro da sojoji da yan sandan domin kawo karshen matsalar. Da yake yiwa manema labarai jawabi Jin kadan da kammala taron a gidan gwamnati dake Yola, Gwamna Fintiri yace za a gudanar da bincike dangane da lamarin domin tabbatar da zaman lafiya da adalci. Yace tattaunawa ya warware matsalar harma hukumomin tsaron sunyi alkawari yin aiki tare domin kare rayuka dama dukiyoyin Al ummar jahar da kasa baki Daya. Gwamna Fintiri ya tabbatar da cewa dukkanin bangarorin biyu sun rasa Jami ansu Daya Daya a lokacin rikicin tare da kira da sukasance suna Kai zuciya nesa domin kaucewa sake aukuwar wannan matsalar. Rikici a tsakanin hukumomin tsaron dai ya fara ne daga Mahadar taget dake cikin karamar hukumar yola ta arewa a jahar Adamawa. Taron ya samu halartan mataimakiyar gwamna Farfesa Kaletapwa Farauta da kwamandan Bataliyar rundunan soji ta 23 dake nan Yola, da kwamishinan Yan sanda dama sauran manyan Jami an gwamnati.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.