Gwamnatin jahar Adamawa ta amince da Karin dubu goma na alawus alawus din masuyiwa kasa hidima a jahar Adamawa

Gwamnatin jihar Adamawa ta amince da karin Naira dubu goma kan alawus alawus na matasa masu yi wa ƙasa hidima da aka turo jahar daga watan Janairun 2024. Gwamnan jahar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ne ya sanar da haka yayin bikin rantsar da matasan na 2023 , rukunin 'BA' tawaga ta biyu wadanda aka turo jahar Adamawa, da ya wakana a sansanin horar da su da ke yankin damare na ƙaramar hukumar Girei. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yace wannan karin kudi da akayi an yi shine domin rage radadin cire tallafi man fetur da gwamantin taraiya ta yi. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya ce babu kuskure gurin turo daliban jahar Adamawa domin yi wa ƙasa hidima, hakan na nan ciki jerin manufofin hukumar na karawa matasan masaniya kan irin taruka da al'adu da ake da su a fadin kasa, a kuma fahimtar da su domin bada tasu gudummawa gurin hadin kai, zaman lafiya da ci gaban kasa. Yayin da yake kara tunatar da su cewa a yanzu aiki yana na da wuyan samuwa, gwamnan ya basu karfin gwiwar yin amfani da duk wani dama da suka samu sakamakon shirin sana'o'in hannu da na dogaro da Kai da aka koyar da su. A nashi jawabi, jami'in kai komo na hukumar dake jahar Adamawa, Mr. Jingi Dennis yace wannan tsarin horar da matasan an kirkiro shi ne domin kimtsa su, gabannin irin rawa da zasu taka gurin bada tasu gudummawa domin ci gaba da kuma gina kasa, da ma nan gaba. Jingi Dennis yace hukumar NYSC ta fara sake duba tsarin aikewa da masu yiwa ƙasa hidima inda take sa ran tura karin matasan zuwa wajen babban fadar jaha domin ganin ba a bar sauran kananan hukumomi a baya ba. Haka shima , shugaban majalisar hukumar ta NYSC na jahar Adamawa, wanda shine komishinan matasa da wasannin, Barristar Wali Yakubu, ya marabci yan bauta kasar tare da kira gare su da su bi duk dokokin sansanin horarwan , su kuma kasance cikin dukkan abubuwa da za a gudanar. Babban alkaliyar jahar, Haphsat Abdulrahaman wanda ta samu wakilcin justis Helen Hammajoda Nuhu ce ta rantsar da su. matasa dubu daya da dari uku da arba'in in ne aka turo jahar.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.