Gwamnatin jahar Adamawa ta amince da bada kwangila gyara hanya da ta tashi daga Damare zuwa Barong.
Gwamnan jahar Adamawa ta amince da bada kwangilar aikin hanya mai tsawon kilomita arba'in da biyu, daga sansanin horar da matasa masu yiwa ƙasa hidima zuwa kauyen borong.
Komishinan ilimi, Doctor Garba Umar Pella ne ya baiyana haka yayin da yayi wa manema labaru jawabi jim kaɗan bayan kammala zaman majalisar jaha karo na takwas wanda gwamnan jaha ya jagoranta.
Doctor Garba Umar Pella yace ganin muhimmancin hanyar wanda ta ratsa tsakanin kananan hukumomin demsa da Girei, gami da irin wahalhalu da mutanen da ke yankin ke sha, gwamnatin jahar taga ya kamata ta bada wannan aikin hanyar.
Garba Pella yace an baiwa kamfanin hydro source and resource Nigeria limited aikin hanyar a kan kudi naira miliyan dari takwas da sittin, da dubu dari takwas da ashirin da biyu da Naira dari uku da talatin, kuma za a kammala cikin watanni goma sha biyu.
Har wayau majalisar ta amince da karin kudin aiki gina dakin gwaji na zamani dake asibitin kwararru dake Yola, kontragi da aka bayar Tun watan Disamban 2021kuma idan aka kammala zai kasance daya daga cikin dakunan gwaji na zamani dake yankin arewacin Najeriya .
A cewar komishinan, an bada kontragin aikin ne a kan kudi naira Miliyan dari biyar da saba'in da takwas, da dubu dari bakwai da bakwai , da Naira talatin da bakwai, da kobo talatin da hudu, kuma aikin ya kai kusan matakin kammalawa amma sai dai majalisar da duba taga yadda kayan gini sukayi tsada shi yasa ta amince da karin kudin.
Doctor Garba Umar Pella yace gwamnati ta amince da wadannan aiyuka ne domin kyautata wa al'ummar jahar Kuma kamar yadda yake kunshe cikin kudirin gwamnatin da fintiri ke jagoranta na sauya yadda ake kallon jahar , da kuma saka ta a jerin jahohi dake gaba gaba a fadin kasa.
Comments
Post a Comment