Gwamnatin jahar Adamawa ta kirayi gwamnatin tarayya da ta Samar da madatsar ruwa a Dasin domin kaucewa Ambaliyar ruwa.

Gwamnan jahar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya kirayi gwamnatin taraiya data samu mafita mai daurewa domin kawo karshen ambaliya da ake fama da shi a fadin kasa. Gwamna Ahamadu Umaru Fintiri yayi wannan kira ne a lokacin da ya karbi bakoncin babban daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA Mustapha Habib Ahmed da wasu jami’an hukumar yayin da suka kawo ziyara a ofishin shi da ke gidan gwamnati a Yola. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yace cikin matakan shawo kan matsaloli da ake fuskanta yayin ambaliya akasa, ya kamata gwamnatin taraiya da gina wani dam a dasin hausa, wanda a cewar shi hakan zai taimaka gurin rike ruwa da ake sako wa daga Lagdo dam na kamaru wanda ke kawo ambaliya ko wani shekara, kuma matsalar ya shafan jahohi da dama a fadin kasa. Gwamna Fintiri yace ya kamata gwamnatin taraiya ta baiwa gina wanna dam din muhimmaci, ganin yin hakan zai taimaka gurin bukasa harkokin noma a fadin kasa. Gwamnan ya kuma yabawa hukumar ta NEMA, da yadda take gaggauta kawo dauki a jahar, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jajar zata ci gaba da baiwa gwamnatin taraiya goyon baya domin ci baga da aikin kai dauki a fadin kasa. A cewar gwamnan, hukumar bada agajin gaggawa ta kasa da ta jaha sun yi asara da dama sakamakon barna da wasu bata gari suka yi a jahar, hakan ne ya sa za a gina dakin ajiya da ofis wa hukumar a cikin harabar gidan gwamnatin. Gwamnan ya kuma kara da cewa nan gaba gwammatin zata gina wasu Karin dakunan ajiyan huda biyu domin kawo karshen sace sacen kayakin NEMA da ake yi. Tun farko dai, babban daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA, Mustafa Habib Ahmed ya jajantawa gwamnan da ma daukacin al’ummar jahar bisa rayuka da aka rasa sakamakon haduran kwale kwale a wasu kauyuka dake jahar. Mustafa Habib Ahmed yace daga yanzu, hukumar NEMA na shirya shiga kwasnce da gwamnatocin jahaohi da wasu cibiyoyin gwamnati domin shirya taron kara wa juna sani kan yadda za kiyaye aukuwar hadurran kwalekwale a cikin al’umma. Babban daraktan ya kuma yi amfani da wannan dama gurin yaba wa gwamnatin jahar adamawa na kasance cikin jahohin farko da suka dau matakin kiyayin ibtila’I daga matakin karkara, ta kuma kafa hukumar kula da aiyukan gaggawa a kananan hukumomi ashirin da daya da take da su, tare da fatan al’ummar jahar sun fara cin moriyar aiyukan su. Ya tabbatar wa gwamnan jahar cewa hukumar NEMA zata ci gaba da bashi goyon baya, inda a guri guda ya gode mishi alkawarin da ya dauka na samar wa hukumar ofisoshin aiyukan ta da dakin ajiya a cikin harabar gidan gwamnatin domin bada kariya da tsaro.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.