Gwamnatin jahar Adamawa yace bazatayi kasa a gwiwaba wajen goyon bayan rundunan yan sanda.
Gwamnan jahar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri yace gwamnatin shi za ta ci gaba da baiwa rundunar yan sanda goyon baya da take bukata domin bata damar sauke nauyin gudanar da aiyukan kare rayuka da kadarori a jahar.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya baiyana hakane yayin da ya karvi bakoncin babban sifeto janar na yan sanda, sKayode Egbetokun, wanda ya ziyarci shi yayin da ya ke ziyaran aiyuka a birnin Yola, fadar jahar Adamawa .
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yace , rundunar yan sandan jahar na kokari matuka gurin kare rayuka da kaddarorin al'ummar jahar Kuma komishinan yan sandan jaha, CP Tola Afolabi na da kokari matuka.
A cewar gwamna fintiri, komishinan yan sandan na kokari gurin hada kai da sauran takwarorin shi na jahar wanda abun yabawa ne kuma zai cigaba da bashi goyon baya da yake bukata domin yin nasara a matsayin shi na jami'in tsaro na farko a jahar.
Yayin da ya baiyana rashin jin dadin shi kan sabani da ya auku tsakanin sojoji da yan sanda a jahar kwanakin baya, gwamnan yace ya kafa wata komitin a matakin gwamnati da za duba sanadin wannan rikici tare da matakan kiyaye aukuwar haka nan gaba.
Gwamnan ya baiwa cibiyoyin tsaro dake jahar tabbacin cewa gwamnatin shi zata basu goyon baya da suke bukata domin cin ma burin su na kare al'umma.
Governor Fintiri yace, yayin ganawar gwamnonin shiryar arewa maso gabas, sun tattauna batun yiwuwar bude sansanin horar da yan sandan danne tarzoma dake goza , da wannan ne ya ne mi izinin babban sifeto janar na ya san dan da ya amince da sake bude wani sansanin a yankin Mbamba domin karfafa tsaro, baiwa jahar damar cin moriyar jagorancin babban sifeton yayin da al'umma ke ci gaba da bashi goyon baya .
Tun farko dai, Babban sifeto janar na yansandan
Kayode Egbetokun yace ya kawo ziyara ne domin godewa gwamnan bisa irin goyon baya da yake baiwa rundunar yan sanda
Kayode yace rundunar zata ci gaba da taimakawa gwamnatin jahar domin ganin an samu zaman lafiya, tare da sauya yadda al'umma ke ganin aikin dan sanda a fadin kasa.
Yayin ziyarar, babban sifeto janar din ya baiwa Gwamna kyauta ta musamman.
Comments
Post a Comment